Gwamnonin Najeriya sun yi wa Aisha Buhari Rubdugu

0

Kungiyar Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa, ba gwamnoni kadai ba ne uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari za ta dora wa laifin cewa al’amurra a kasar nan ‘sun fara shiga gargara, ga kuma gwamnatoci ba su yin komai.

Aisha Buhari, wadda a baya ta sha sukar bangarorin gwamnatin Buhari daban-daban, a wannan karon kuma gwamnoni ta ragargaza, tare da cewa yawancin al’ummar karkara ba su samun ruwan sha a jihohin su.

“Ya za a ce wai mu na da gwamnoni a kasar nan, amma dan ruwan da al’umma za su sha ma a cikin karkara ya na gagarar su.” Haka ta bayyana a ranar Juma’a, a wurin Taron Majalisar Koli ta Musulunci ta Najeriya, da aka gudanar a Abuja.

Sai dai kuma Kungiyar Gwamnonin Arewa ta kasa daurewa, har ta maida wa Aisha raddi, wadda kakakin kungiyar, Abdulrazaque Barkindo ya sa wa hannu a jiya Lahadi, cewa duk wani bayanin da Aisha ta yi da ta danganta da gwamnonin, ba “gaskiya ba ne, kuma kage ne kawai.”

Barkindo ya ce kowane gwamna a fadin kasar nan ya na kokari da kuma aiki ba dare, ba rana wajen tabbatar da inganta rayuwar milyoyin jama’ar da ke karkashin sa, domin fitar da su daga kuncin rayuwa, fatara da talauci.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari cikin watan Nuwamba, cewa Kungiyar Gwamnonin Arewa ta kaddamar da gagarimin shirin Inganta Rayuwar Al’aumma, wanda nan da shekarar 2030 za su cito mutane milyan 24 daga kuncin talauci da fatara.

Wannan shiri ne da aka kirkairo a karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.

“Gwamnonin jihohin kasar nan su na nan na ta yin iyakar kokarin su don ganin sun fitar da milyoyin ‘yan Najeriya daga kuncin talauci.

“Don haka ba daidai ba ne labarin da aka lakanta da Aisha Buhari, da aka ce ta yi wa gwamnoni korafin rashin tabuka abin kirki wajen samar da ruwan sha a yankunan karkara da kuma inganta rayuwar talakawa.” Haka Kungiyar Gwamnoni ta Kasa ta bayyana.

Daga nan sai kuniyar da aka fi sani da suna NGF ta ce dukkan wasu masu rike da shugabancin siyasa “sun damu da bayanin da Aisha Buhari ta yi, ba ma gwamnoni kadai ba.”

Sanarwar ta ce furucin wanda ake ta alakantawa da gwamnoni ne ke da laifin kowane irin kunci ko matsala da talakawan karkara ke ciki, kamar yadda ta yi magana a kan batun ruwan sha, tamkar ana nuna cewa gwamnonin za su hadu da fushin Alla ne kenan. Musamman idan aka yi la’akari da wurin da ta yi jawabin, wato wurin Taron Majalisar Kolin Harkokin Musulunci ta Najeriya.

Share.

game da Author