SALWANTAR KUDADE: El-Rufai bai taba hana EFCC gudanar da aikin ta ba

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bai taba yunkurin hana EFCC gudanar da bincike a kan sa ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka yi zargin haka.

Maimakon haka, lauyan gwamnan ya yi karin haske cewa, a duk lokacin da aka zargi El-Rufai, shi kotu ya ke garzayawa, inda a can ne ya ke kare kan sa.

Cikin wata sanarwa da lauyan sa AU Mustapha ya fitar, ya ce a 2009 EFCC ta yi kokarun shafa wa El-Rufai kashin kaji, amma sai ya je kotu ya kare kan sa.

Wannan martani ya biyo bayan labarai da sharhin da aka rika watsawa ne, sakamakon mummunar fahimta da aka yi wa wani hukunci da Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke, inda aka rika yi wa El-Rufai kallon wani wanda ya hana EFCC gudanar da aikin ta.

“Ko sau daya El-Rufai bai taba hana EFCC gudanar da aikin ta ba. Cikin 2009 ya garzaya kotu inda ya kare kan sa, saboda a lokacin EFCC ta dauko baudaddiyar hanyar neman bata masa suna ta hanyar watsa bayanai da gulmace-gulmace a kan sa, maimakon ta yi bincike.” Cewar lauyan sa.

“EFCC ta rika kamfen din bata masa suna a cikin 2009, wai wasu zunzurutun kudade, har naira bilyan 32 sun salwanta a hannun sa. Dalili haka El-Rufai ya garzaya kotu, ya je ya kare kan sa. Kuma kotu ta tabbatar da cewa ya na da gaskiya, bai salwantar da wadannan kudade ba.”

Mustapha ya ce fitowar da ya yi a yanzu ya yi bayani dalla-dalla, ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke ne a wata kara, a ranar 29 Ga Nuwamba, 2019.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a lokacin da El-Rufai ke Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya raba filaye 27,000, kuma duk kan ka’ida, sannan kuma ya tara naira bilyan 32 na kudaden da ya raba filayen.

Mustapha ya ce El-Rufai bai ci ko sisi a cikin kudin ba, ya saka kudaden aljihun Gwamnatin Tarayya.

Mustapha ya ce kasancewa duk wani mutumin kirki ba zai zura ido ana bata masa suna, kamar yadda EFCC ta bari ana amfani da siyasa ana bata sunayen mutane ba, sai El-Rufai shi ma ya je kotu, aka wanke shi fes.

Share.

game da Author