Ba zan sake tsayawa takarar zabe ba – Goje

0

Sanata Danjuma Goje ya bayyana cewa daga wannan zaben na 2019 da aka yi masa, ba zai sake fitowa takarar neman zabe a kowane mukami ba.

Goje wanda ya taba yin gwamna a jihar Gombe tsakanin 2003 zuwa 2011, ya bayyana haka a lokacin da ya kaddamar da tallafi a Filin Wasa na Pantami a ranar Asabar da ta gabata.

Sai dai kuma ya ce hakan ba wai ya na nufin ya yi bankwana da siyasa ba har abada.

Goje ya ce ya na cikin jam’iyyar APC, amma dai zai ja baya ya bayar da fili ga masu jiki a jika, su ma su gwada basirar da Allah ya basu.

Goje ya ce zai ci gaba da siyasa amma a matsayin dattijo, ba dan takara ba.

“Sau bakwai ina tsayawa takara, kuma sau bakwai ina yin nasara. Ina ganin ba kowane dan siyasa Allah ya bai wa irin wannan damar da ya ba ni ba.

“Don haka ina sanar wa jama’a zan daina fitowa kowace irin takara. Amma dai ina cikin siyasa tsundum, ba fita zan yi ba.

“Za ni ba masu jini a jika fili domin su ma su shigo su bayar da ta su basirar. Amma dai ni, ai shekaru na sun ja sosai, don haka ba zan sake tsayawa takara ba.

“Na fara takara tun a zamanin mulkin Shagari, inda na tsaya takarar dan majalisar jihar Bauchi, kuma na yi nasara.

“Na yi takarar Sanata zamanin mulkin Abacha, inda na wakilci jihar Gombe ta tsakiya. Sannan kuma na yi takarar Gwamna sau biyu, ga shi kuma ina zangon sanata na uku kenan.

Dubban jama’a ne suka halarci taron da aka gudanar a Filin Wasa na Pantami, a Gombe.

Share.

game da Author