Manoman shinkafa sun roki gwamnati ta kara garkame kan iyakoki

0

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya, RIFAN ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da kara garkame kan iyakokin kasar nan.

RIFAN ta ce rufe kan iyakokin Najeriya zai kara karfafa tattalin arzikin kasar nan.

Shugaban Kungiyar RIFAN na Jihar Neja, Idris Abini ne ya yi wannan kira a Minna, a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai jiya Lahadi.

Abini ya kara da cewa rufe kan iyakoki ya kara yawan shinkafar da ake nomawa a jihar Minna saboda yawan bukata da neman shinkafar da ‘yan kasuwa da kuma masu saye su ci ke yi.

“Amma kuma dai har yanzu ba mu kai ga noma shinkafar da jama’a ke bukata ba, saboda bukatar shinkafar ya karu sosai.

“Duk da haka mun kama hanyar kara noma shinkafa mai tarin yawan gaske, saboda kulle kan iyakokin kasar nan da aka yi.

“Rufe kan iyakoki abu ne mai kyau kwarai, saboda tuni alheri da albarkar noma na ta baibaye manoma shinkafa. Saboda yanzu jama’a sun koma cin shinkafar cikin gida wadda mu ke nomawa.

Abini ya ce akwai iri daban-daban na shinkafa masu nagartar da ke iya gogayya da shinkafar da ake shigowa da ita daka kasashen waje.

Sannan kuma shugaban na RIFAN ya ce rufe kan niyakokin zai tasayar da shigo da muggan makamai barkatai da ake yi a cikin kasar nan.

“Masu sukar rufe kan iyakokin kasar nan ba cikakkun ‘yan Najeriya ba ne, saboda rufewar na daya daga cikin alherin da wannan gwamnatin ta bijiro mana da su.

Idan za a iya tunawa, tun cikin Agusta gwamnatin tarayya ta kulle kan iyakokin kasar nan, bisa dalilin kyalewar da kasashen ke yi ana shigo da kayan sumogal cikin Najeriya ba tare da kasar na samun kudaden shiga ba.

Najeriya ta nuna matukar damuwa yadda masu shigowa da kaya cikin kasa ba su sauke kayan su a tashoshin jiragen ruwa na Legas.

Maimakon haka, sai su sauke a tashar ruwa ta Kwanato, daga nan a rika yin fasa kwaurin kayan zuwa cikin Najeriya, ba tare da ta samu makudan kudaden shiga ba.

Cikin makon da ya gabata ne kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu ranar sake bude kan iyakoki, har sai al’amurra sun gyaru tukunna.

Tuni dai Najeriya ke ikirarin cewa kudaden shiga na ta karuwa sakamakon rufe kan iyakoki da aka yi.

Share.

game da Author