SHAN-INNA: ERC za ta tantance Najeriya don bata shaidar yin sallama da cutar

0

Kodinatan shirin yi wa yara allurar rigakafi a karkashin inuwar hukumar WHO Pascal Mkand ya ce Najeriya za ta iya samun shaidar rabuwa da shan inna kwata-kwata idan daga yanzu zuwa karshen shekaran 2020 ba a samu rahoton bullowar cutar a kasar ba.

Mkanda yace hakan zai tabbata ne idan kwamitin ERC ta gamsu da ingancin kokarin kawar da cutar da gwamnatin kasar take yi.

Ya ce kwamitin za ta fara gudanar da bincike akai daga mako mai zuwa.

Mkanda ya fadi haka ne a taron inganta hanyoyin kawar da cutar da yi wa yara allurar rigakafi a Nahiyar Afrika da aka yi a Abuja a makon jiya.

Ya jinjina kokarin da fannin kiwon lafiyar Najeriya ke yi wajen dakile yaduwar cutar.Sannan ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta mai da hankali wajen dakile yaduwar shan-inna a kasar.

Sakamakon binciken da jami’an kiwon lafiya suka gudanar ya nuna cewa wata sabuwar cutar shan inna mai suna ‘Circulatin Vaccine-Derived Poliovirus’ ya bullo sannan har ya fara kareda kasashen Afrika guda 12.

Wadannan kasashe sun hada da Angola,Benin,Kamaru Afrika ta Tsakiya Jamhuriyar Chadi,Jamhuriyar Kongo,Ethiopia,Ghana,Nijar,Najeriya,Togo da Zambiya.

Jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa mutum na kamuwa da wannan cuta ne idan akwai kwayoyin cutar shan inna a jikinsa kuma ya yi allurar rigakafin cutar.

Sannan yawan zama a muhalli mara tsafta da rashin samun ingantaccen kiwon lafiya, rashin yin allurar rigakafin cutar na daga cikin hanyoyin kamuwa da ita.

Kwamitin ERC ta gargadi gwamnatin Najeriya da ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta dakile yaduwar wannan cuta.

Idan ba a manta ba a taron samar da makawar shan-inna da aka yi a Abuja a watan Agustan da ya gabata ne shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakon farko na Najeriya (NPHCDA) Faisal Shu’aib ya ce Najeriya ta maida hankali matuka domin ganin ta samu shaidar yin sallama da shan inna kwata-kwata a kasar.

Shu’aib ya ce kwamitin ERC na bada wannan shaida ne ga duk kasar da ta yi akalla shekaru uku basu samu rahoton bullowar cutar a ko ina ba.

Share.

game da Author