Ba zan je taron sasantawar ‘shirmen’ da Yari ya shirya a Zamfara ba –Kabiru Marafa

0

Tsohon Sanatan Jihar Zamfara, Kabir Marafa, ya nesanta kan sa daga taron neman sasantawa da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya shirya yi da gungun ‘yan jam’iyyar APC ‘yan G-8 din da ya samu sabanin siyasa da su kafin zaben 2019.

Kakakin Yada Labarai na APC reshen Jihar Zamfara, Shenu Isah, ya shaida wa manema labarai a Gusau cewa wannan kungiyar ta G-8 ta yunkuro da nufin sasanta kazamin rikicin da ya tirnike har ya haddasa APC ta rasa dukkan mukamai a zaben 2019 na jihar Zamfara.

Kungiyar Mashahuran G-8 na Zamfara, sun hada da Kabiru Marafa, Dauda Lawal, Ibrahim Wakkala, Mahmud Shinkafi da Aminu Sani da sauran su.

Ya ce sun tattauna matsalolin da APC ta fuskanta a lokacin hauma-haumar zaben 2019, kuma sun cimma amincewar zama su magance matsalolin.

Sai dai kuma a na sa bangaren, Marafa ya ce shi dai ba ya “cikin wannan kwaram-da-hama da sunan taron sasantawa.”

Sannan kuma ya ce shi dai babu wanda ya sanar da shi akwai wani taron sasantawa, kuma ko da an sanar da shi din, to bai ga dalilin zuwa ba.

Marafa ya ce tun farko Yari ne ya ki amincewa a zauna a magance matsalar tun kafin zabe, duk kuwa da kokarin da uwar jam’iyya, fadar shugaban kasa da manyan ‘yan siyasa suka yi domin jawo hankalin sa.

Marafa ya ce a lokacin Yari ya na jin kan sa, ya na tutiya da tinkahon cewa shi ne gwamnan Zamfara, kuma ya na da kudaden Zamfara na da Kungiyar Gwamnonin Najeriya a hannun sa, sai yadda ya ga dama ya rika yi.

“A lokacin ya je ya samu hukuncin baubawan-burmi daga Kotun Jiha, wanda Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli suka yi fatali da shi.

“A yanzu kuma ya ga ba shi da karfin mulki a hannun sa, Allah ya wofintar da shi, jama’a kuma sun juya masa baya, shi ne a yanzu ya ke ta kokarin shirya wani taron ihu-bayan-hari, domin ya sake farfado da tagomashin sa.

“Tun farko shi ne ya ki yarda ya saurari kiraye-kirayen da jama’a masu tunani da hangen nesa suka rika yi masa, wanda da a lokacin ya tsaya ya saurara, da shawarwarin sun amfani jama’ar mu da jam’iyyar mu baki daya.” Inji Marfa.

“Yari ne ya haifar da dukkan matsalolin da suka haifar wa APC mummnunar asara a Jihar Zamfara, saboda ya rika daukar kan sa wani ubangiji, mai girman kai, saboda kawai tantagaryar jahilci ya yi masa katutu. Alhali kuwa ba komai ba ne, kuma ba kowa ba ne. Dama holoko ne, kuma tubalin-toka.”

Share.

game da Author