El-Rufai na mulkin Kaduna kamar wata karamar Najeriya – Inji Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yabawa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai bisa kokari da maida hankali da yayi wajen canja fasalin jihar Kaduna zuwa jihar da za’a rika alfahari da ita a Najeriya.

Obasanjo ya bayyana haka ne da ya ke jawabi a fadar gwamnatin Kaduna a ziyarar gaisuwa da ya kai wa gwamnan El-Rufai.

” Na yi zama a Kaduna daga 1959 zuwa 1967 a dalilin aikin Soja a wancan lokaci. Bayan haka kuma ina so kowa ya sani cewa a Kaduna na fara gina gidan zama na na kai na Unguwar Makera.

Obasanjo ya kuranta El-Rufai cewa shi jarumi ne wadda aiki kawai ya saka a gaba a duk inda yake. ” Yayi matukar nuna bajintar sa a lokacin da yake ministan Abuja kuma ina alfahari dashi, domin yayi abinda wasu da dama baza su iya yi ba. Ina taya mutanen Kaduna murnar samun jarumi irin Nasir El-Rufai a matsayin gwamna.

” Najeriya na bukatar mutane irin Nasir El-Rufai da aka san irin abinda zai iya yi. El-Rufai dan baiwa ne, kawai ku sani.

A nashi jawabin, El-Rufai ya ce ya koyi dabarun aikin gwamnati ne a lokacin da yake aiki a karkashin shugaba Obasanjo.

” Obasanjo ya koya min dabarun aikin gwamnati a lokacin da nake aiki a karkashinsa. Ina matukar yi masa godiya da wannan ziyara da ya kawo jihar Kaduna.

Share.

game da Author