Dan Afrika ba ya bukatar bizar shiga Najeriya – Inji Buhari

0

Shugaba Muhammadu buhari ya bayyana cewa daga watan Janairu 2020, duk wani dan Afrika zai rika karbar biza a daidai inda ya shiga kasar kai tsaye.

Ya yi wannan bayani a garin Aswan, cikin kasar Masar, inda ake kammala taron neman makamar inganta tattalin arzikin kasashen Afrika, wato Aswan Forum.

“Mu a Najeriya tuni muka dauki matakin ruguza duk wani bangon da ya yi mana kandagarki da sauran kasashen Afrika, wanda ke kawo cikas wajen zirga-zirgar jama’a.

“Don haka duk dan Afrika da ke da fasfo din kasar sa rike a hannu, zai iya shigowa Najeriya ba tare da biza ba, sai ya zo wurin shiga nan take a yi masa bain sa, ya karba.

“Daga watan Disamba, 2019 an daina wahalar neman biza, domin daga watan Janairu, 2020 za mu fara aiki da wannan sabon tsari.” Inji Buhari a lokacin da ya ke jawabi.

Tun bayan fara shigo da wannan tsari, a cikin watan Yuli an bai wa masu shigowa Najeriya su sama da 2000 da nufin zuba jari bizar su a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Lagos.

Buhari ya ci gaba da cewa akwai matukar bukatar a kawo karshen rikice-rikice a Afrika. Domin kamar yadda ya kara yin nuni, wadannan rikice-rikice su ne ke haifar mana da matsalolin da ke zame mana tarnaki da dabaibayin da ke hana Afrika ci gaba.

Cikin jawabin na sa mai take, “Muhimmancin Zaman Lafiya Da Ci Gaba”, Buhari ya kara jaddada cewa zaman lafiya na gaba da komai, domin sai da zaman lafiya ake iya samun ci gaba da inganta tattalin arziki.

Wannan taro da Buhari ya fita zuwa Masar, shi ne fitar sa ta 12, tun bayan sake rantsar da shi karo na biyu a ranar 29 Ga Mayu, 2019.

Buhari ya kuma nuna muhimmancin gina titinan motoci da na jiragen kasa da za su rika bulla daga wannan kasa zuwa waccan, da nufin zaukaka zirga-zirgar kasuwanci tsakanin kasashe makwauta da na nesa a cikain Afrika.

Ranar Juma’a ce ake sa ran komawar Buhari Abuja.

Share.

game da Author