Gwamna Yahaya Bello da aka sake zabe karo na biyu a Jihar Kogi, ya maida wa PDP martanin cewa shi da jam’iyyar sa APC sun yi kyakkyawan shirin duk irin kokawar da za a yi a gaban shari’a domin kare nasarar sake zaben sa da ya ce ya yi.
Gwamnan ya furta haka a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, lokacin da ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a Fadar Shugaban Kasa, a jiya Alhamis a Abuja.
Jami’in Zabe Farfesa Ibrahim Garba, ya bayyana cewa Bello ya lashe kuri’u 406,222, shi kuma abokain adawa, Musa Wada, ya samu 189,704.
Sai dai kuma ko da sauran jam’iyyu 22 sun hakura, jam’iyyar PDP da SDP sun ce ba su yarda ba, an yi ta’addanci da satar kuri’u a wurare da dama.
Bello ya ce damka masa satifiket na shaidar lashe zabe da INEC ta yi, ya tabbatar da cewa nasarar da ya samu ba ta da wata matsala kenan.
“Dazun nan ba da dadewa ba na karbin satifiket daga hannun INEC. Wannan karbar kati kuwa shi ne karshen ayyukan zaben gwamna da aka gudanar a ranar 16 Ga Nuwamba, 2019.
“Ni fa batun yau ba, tuni na shaida muku cewa ba na tantamar sake lashe zabe. Kuma na san zan yi wa dan takarar PDP rata mai yawan da ko ma da ya je kotu, to babu wata madogara da zai iya tinkaho da ita don gabatar da wasu hujjoji.
“Amma fa ba hana shi zuwa kotu na yi ba. PDP na da ‘yancin zuwa kotu, idan za su je. Za mu hadu a can.
“Amma kuma wannan ba zai hana ni yin kira ga dukkan wadanda suka yin takara da ni ba, tun daga zaben fidda gwani har zuwa babban zaben gwamna, cewa dukkan mu ‘yan jihar Kogi ne. Don haka su zo mu hadu mu kara ciyar da jihar mu gaba.
Bello ya ce ya gaji dadaddiyar matsalar kabilanci a jihar Kogi, amma saboda ya himmatu kwarai, sai da ya magance matsalar.
Sannan kuma ya ce nasarar zaben da ya samu, ta kara tabbatar da cewa matsalar kabilanci ta kusa zama tarihi a Jihar Kogi.
“Da yardar Allah, tun daga wannan zaben, an binne matsalar kabilanci a Jihar Kogi. Saboda babu shiyyar da ban samu kuri’u masu tarin yawa ba.”
Discussion about this post