Yadda Abubakar ya bindige matar kawunsa Fatima saboda zargin maita

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tsare wani matashi mai suna Abbas Abubakar da ta kama da laifin kashe matar kawunsa mai suna Fatima Maitala.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Isaac Akinmoyede ya sanar da haka ranar Alhamis yana mai cewa Abubakar ya aikata wannan laifi ne a kauyen Kissayip dake karamar hukumar Bassa.

Ya ce ‘yan sanda sun samu labarin aika-aikan da Abubakar ya yi ne daga bakin kawunsa Maitala Bako.

Akinmoyede ya ce Abubakar mai shekaru 29 ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa shine ya kashe Fatima da bindiga.

“ Abubakar ya ce Fatima ce ta kashe wani kawunsa, ta kuma kashe bujimin san da yake kiwo sannan ta yi barazanar kashe shi da duk sauran mutanen dake gidan su. Yana zarginta da cewa ita matsafiyace kuma ta na maita.

A dalilin haka sai yaga kawai buri ya riga aikata lahira kafin ta illatashi. Bayan an kamashi kuma ya bayyana yadda ya kashe matar kawun nansa sai ya nuna yin nadama bisa abinda ya aikata sannan ya mika ya ‘yan sanda bindigar da ya harbe ta.

Saidai kuma dama can shi wannan matashi, wato Abubakar na daya daga cikin batagari 36 da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo a jihar.

Ana farautar su bisa aikata muggan laifuka da suka hada da fyade, kisa, garkuwa da mutane, shan miyagun kwayoyi da sauran su.

Share.

game da Author