Rashin kula da ni da mijina baya yi ya sa na jefar da jaririyar mu a masai

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wata mata mai suna Amudalat Taiwo da aka samu ta jefa jaririyar da ta haifa a cikin masai.

Kakakin ‘yan sandan Abimbola Oyeyemi wanda ya sanar da haka ya ce sun damke Amudalat ranar Litini ne a lokacin da suke gudanar da bincike akan wannan abu da ta yi.

Oyeyemi yace binciken da suka gudanar ya nuna cewa Amudalat ta haifi wannan jaririya ce kwanaki 12 da suka gabata sannan a ranar Larabar da ta gabata haka nan kawai sai ta jefata a cikin masai.

“Mai gidan hayan da Amudalat ke zama ne ya garzayo ofishin mu ya sanar da mu cewa sun ji kukan jariri a cikin wannan masai.

“Mai gidan yace wata mata ne dake gidan ta fita da sassafe domin ta zaga inda kawai ta ji kukan jariri. Nan da nan kuwa muka fasa masan muka ciro jaririn.

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Amudalat marainiya ce. Ta jefa jaririyar ne saboda yunwa da rashin kula daga wajen mijinta,

“Amudalat ta ce ta auri wani mutum mai suna Taiwo Owolabi inda bayan auren su ya koma wa uwar gidan sa sannan ita ya daina kula da ita.

Oyeyemi yace a yanzu haka Owolabi na tsare a ofishin su sannan da zaran sun kammala bincike za su maka Amudalat da mijinta a kotu.

Share.

game da Author