Daidai misalin karfe 10 na dare, jiya Asabar, wasu mahara dauke da muggan makamai suka dira garin Ugwolawo, cikin Karamar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi, suka tarwatsa ma’aikatan zabe da masu aikin sa-ido kan zabe da suka samu a ofishin.
Wannan al’amari ya faru a daidai lokacin da ake tattara sakamakon zabe. Maharan dai sun yi ikirarin cewa wai daga Zamfara suke.
Sun shafe sama da awa daya a garin su na harbi-harbe a sama. An kuma tabbatar da cewa sun gwabza arangama da ‘yan sanda, wadanda suka kai dauki ofishin daga baya.
Sun rika kakabin cewa duk mutanen garin kowa ya zauna gidan sa, kada wanda ya sake fitowa wurin tattara sakamakon zabe a ofishin INEC.
Wakilin mu da sauran masu sa-ido kan zabe da ke ofis din, lamarin ya ritsa da su, sai da ta kai sun arce, sun afka cikin wani gida suka kwanta har bayan sa’a daya.
Har zuwa lokacin da wakilin mu ya fito jiya tsakar dare ya aiko da wannan rahoto, wasu mazauna garin da masu sa-ido kan zabe na can a boye cikin gidajen mutane, ba su fito ba.
An yi kokarin jin ta bakin jami’in INEC kafin buga wannan labari.