Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, ya samu nasarar lashe zabe a Karamar Hukumar sa ta Okene da kuri’u 112,764.
Shi kuma Musa Wada na PDP ya samu kuri’u 139 kacal.
Ita kuwa ’yar takarar jam’iyyar SDP, Natasha Akpoti, ta samu kuri’u 50 tal.
Wannan sakamakon zabe dai jami’in tattara sakamako na Karamar Hukumar Okene, Farfesa Olanrewaju Samuel ne ya sa masa hannu.
An yi tsammanin jam’iyyun uku za su samu kuri’u masu tarin yawa, ko da bas u kai na Bello ba.
Sai ga shi yawan adadin kuri’un da INEC ta ce PDP da SDP sun samu, ba su kai 200 ba ma.
Wannan lamari ya bayar da mamaki, tuni dai Natasha ta yi Allah wadai da sakamakon zaben. Dama kuma tun farko ta ce yaki aka yi a Shiyyar Mazabar ta Kogi ta Tsakiya ba zabe ba.
Masu lura da al’amuran siyasa sun cika da mamaki, musamman ganin yadda PDP da Natasha ke da jama’a a Karamar Hukumar.
Idan ba a manta ba, a zaben 2015, Natasha ta tsaya takarar sanata, inda ta samu kuri’a sama da 48,000. Dalili kenan ake ganin bai yiwuwa a ce a garin haihuwar ta ta ci kuri’u 50 kadai.
Yayin da PDP ta yi watsi da sakamakon zaben, jama’a da dama na nuna damuwar su dangane da yawan tashe-tashen hankulan da suka hada har da kisa da suka rika faruwa kafin ranar zabe a kuma ranar zabe.
An koka kwarai da yawan satar akwatinan zabe da kuma fasa taron masu zabe, da kekketa takardun zabe.
Idan ba a manta, ita kan ta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ta rasa inda ma’aikatan ta har 30 sun bata.
Wasu da dama sun rika nuna cewa bai kamata a bai wa Gwamna Yahaya Bello naira bilyan 10 ana saura kwanaki biyu zaben gwamna ba.
Discussion about this post