Sojojin Nakeriya sun kubutar da mutane takwas dake tsare a hannun Boko Haram

0

Dakarun sojin Najeriya dake aiki a karamar hukumar Gwoza jihar Barno sun kubutar da mutane takwas dake tsare a hannu Boko Haram.

Kakakin rundunar Aminu Iliyasu ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi.

Iliyasu ya ce dakarun sun samu wannan nasara ne bayan arangamar da suka yi da Boko Haram a gwoza ranar Asabar.

Ya ce sun ceto mata hudu wanda a ciki akwai wata tsohuwa sannan da yara hudu.

“Sauran Boko Haram din da suka tsira da ransu sun gudu zuwa tsaunin Madara da raunin harsashi.

“Mun yi wa yaran kananan allurar rigakafin shan inna sannan muna kuma kula da tsohuwan dake tare da su.

Share.

game da Author