Majalisar Dattawa za ta kakaba wa ’yan soshiyal midiya takunkumi

0

Majalisar Dattawa ta sake kakkabe kurar da ke kan kwafen kudirin dokar kakaba wa ‘yan soshiyal midiya takunkumi a Najeriya.
Ranar Talata ce aka sake gabatar da kudirin a zauren majalisa.

Wanda ya bijiro da wannan kudiri ya bayyana cewa idan aka amince da shi ya zama doka, zai magance matsalar watsa labaran karya a kafafen soshiyal midiya.

Sanata Sani Mohammed Musa ne ya gabatar da kudirin, kuma ya na cikin kudirori 11 da aka karanta tun da farko.

Ko a zamanin Majalisar Dattawa Zango na 8, an yi kokarin shigar da kudirin taka wa ‘yan soshiyal midiya burki, amma ba a yi nasara ba.

Shugaban Majalisar Dattawa na lokacin, Bukola Saraki na daga cikin wadanda ba su goyi da bayan kudiri ba. kuma ya ce ba za su amince da shi ba.

A wancan lokacin Sanata Bala Ibn Na’Allah ne ya gabatar da kudirin a Majalisar Dattawa.

Wani bangaren kudirin ya bayyana cewa: “Duk wanda ya yi gangancin buga labarin karya to za a kulle shi watanni shida.”

Akwai kuma wani bangaren da ya nuna za a iya cikin mutum tarar naira 2,000,000 ko zaman kurkukun shekaru biyu.

A lokacin har an karanta kudirin sau biyu a Majalisar Dattawa, amma sai Buhari ya nesanta kan sa da shi, ya ce shi ya yi amanna da ‘yancin fadar albarkacin bakin jama’a.

Tsohon Kudiri

Da an kai ga sa wa kudirin hannu, to duk wanda aka kama ya watsa ko ya rubuta karya a shafin Facebook, Twitter, Instagram da sauran shafukan soshiyal midiya, za a ci shi tarar naira milyan biyu ko daurin shekaru biyu.

Shi kuma wannan sabon kudiri kamar yadda Sani Musa wanda ya gabatar da shi ya bayyana, ya ce zai taimaka wajen tsabtace soshiyal midiya.

Sabon kudiri

A cewar sa zai kawo karshen yadda mutum haka kawai zai shiga dakin sa ya zauna, ya rubuta karairayi da sharri a kan wani ko wasu mutane ya watsa a soshiyal midiya saboda bata suna.

“Ni ina ganin mu na da bukatar dokar soshiyal midiya a nan kasar. Idan har kasashe irin Philippines, Singapore, Italy, Australia, Faransa, Indonesia da Egypt sun kafa irin wadannan dokoki, babu abin da ai hana mu ma a nan kasar mu kafa.” Inji Sanata Musa.

Ya ce idan ba a koya wa mutane hankali ba, to a haka za su rika wuce-makadi-da-rawa a soshiyal midiya sun a kantara wa mutane karya da tozarta su.

“Idan har wani haka kawai zai kirkiri karya ya watsa hoton shugaban kasa da ya lika tare da hoton wata, ya ce katin sanarwar bukin auren su ne, to ni dai ina ganin wannan tozarta ofishi ne da kuma girman mukamin shugaban kasa.”

Hukunci Kan ‘Yan Soshiyal Midiya

“Wanda aka kama ya na watsa irin wadannan bayanai na kirkirar karairayi, za a ci shi tarar naira 150,000 ko kuma daurin shekaru uku, ko kuma idan ya nuna izgilanci, a gada masa duk biyun a lokaci guda.

“Idan kuma kafar yada labarai ce aka sanar da ita cewa abin da ta watsa ba daidai ba ne, kuma ta ci cirewa, to za a ci ta tarar naira milyan biyar, har zuwa naira milyan 10.

Share.

game da Author