Shugaban Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) Farancis Faduyile ya bayyana wasu dalilai da ce sune suke sa ma’aikatan kiwon lafiya ke yawan yin sakaci da aiyukkansu a asibitocin kasar nan.
Faduyile ya ce rashin isassun ma’aikata, rashin ingantattun kayan aiki, rashin isassun asibitoci da rashin albashi mai tsoka na cikin matsalolin dake haddasa haka a fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Ya fadi haka ne a hedikwantar kungiyar dake Abuja.
Faduyile yace aiki na yi wa ma’aikatan kiwon lafiya yawa a dalilin rashi isassun ma’aikata a asibitoci.
“Ma’aikatan fannin kiwon lafiyar kasar nan na daga cikin kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da ake tunkaho dasu a duniya sai dai kash, a na samun baraka ne a dalilin karanci da suka yi da hakan ke sa su rika yin wasu abubuwa ga marasa lafiya da bai kamata ba.
Ya kuma yi kira ga mutane da su rika saurin kai karan duk wani ma’aikacin kiwon lafiyar da suka tabbatar da gangar ne yake sakaci da aikinsa a asibiti.
Ya ce gwamnati ta kafa kotu domin hukunta duk ma’aikacin da aka samu yana yin yadda ya ga dama a aikin sa ko kuma wulakanta marasa lafiya.
Faduyile yace baya ga wannan kotu sai kuma babbar kotun kasa ce ke da ikon hukunta duk ma’aikacin kiwon lafiyar da ya yi sakaci da aikinsa.
Discussion about this post