Majalisar Dattawa ta dibga abin mamaki a jiya Labara, yayin da mambobin ta suka amince aka yi wa kudirin dokar kara Harajin Jiki Magayi, wato ‘VAT’, daga kashi 5 bisa 100 zuwa kashi 7.5 bisa 100, ba tare da sun san takamaimen abin da kudirin ya kunsa ba.
Karanta kudirin da aka yi a zauren Majalisar Dattijai jiya Laraba, shi ne karo na biyu, kasancewa ranar Talata aka fara karanta shi.
Amma dai Sanatoci biyu sun yi korafin cewa bai kamata a karanta kudirin dokar da dattawan majalisar ba su fahimci abin da ya kunsa ba.
Sai dai kuma Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya gwasale su, ya ki amincewa da korafin na su.
Wannan kudirin doka na karin kudin ‘VAT’ da Gwamnatin Tarayya za ta kara dai ba a ma raba wa ko sanata daya kwafen sa ba, ballanata har kowanen su ya je ya yi duba da nazarin abin da ya kunsa.
Sanata Binos Yaroe, na Shiyyar Adamawa ta Kudu kuma dan PDPne ya fara tashi ya yi korafi da tsokacin cewa doka ta haramta a karanta kudirin wata doka da Shugaban Kasa ke so a sa mata hannu ba tare da an gabatar da kwafen kudirin ga kowane sanata ya yi nazarin ta ba.
“Ta yaya za’a karanta mana kudirin da babu ko daya daga cikin mu da suka ga kwafen sa aka damka wa kudirin ballantana mu je mu yi nazari kafin mu tattauna shi a zauren majalisa. Idan ku an ba ku kwafe, to ni dai babu wanda ya ba ni.” Inji Yaroe.
Ita ma Sanata Betty Afiapi, ‘yar PDP daga Jihar Rivers, ba ta gamsu ba, ta yi korafi iri daya da wanda Sanata Yaroe ya yi.
Amma Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Abdullahi Yahaya, cewa ya yi wannan karin kudin haraji na ‘VAT’ zai zama alheri ga gwamnatin tarayya, domin za ta kara samun kudaden shiga masu yawa.
Wasu sanatocin da suka yaba da karfin kudin Harajin Jiki Magayi, sun hada da Ibrahim Gobir daga Sokoto, Istifanus Gyang daga Filato, Buhari Abdulfatah, Oyo, George Sekibo, Rivers da kuma Sahabi Ya’u daga Zamfara.
Daga cikin wadanda suka goyi bayan karin kudaden harajin, babu ko sanata kwaya daya tal da ya ce ya ga kwafen kudirin, ballantana ya yi ikirarin ya karanta, har ya yi inkarin alfanu ko rashin alfanun sa.