Jam’iyyar APC reshen Jihar Akwa Ibom, ta nemi a tsige Ministan Harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio daga mukamin sa.
Cikin wata takarda da Shugaban APC na Jihar Akwa Ibom da Sakataren sa Ali Dolari da Ben Nwoye suka sa wa hannu, sun ce ba su ga amfanin dan jihar su, Akpabio a kan mukamin ba.
Sun zarge shi da yin katsalandan a harkokin Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).
APC ta ce Akpabio ya wuce makadi da rawa inda ya yi shisshigin nada wa hukumar Manajan Darakta, wanda dokar Najeriya ta haramta a nada shi.
Akpabio ya nada wani makusancin sa mai suna Dakta Cain Ojogboh, wanda likita ne, a matsayain Daraktan Riko mai Kula da Kwangiloli, alhali kuma likita ne.
Dokar da ta kafa NDDC dai ta ce sai kwararren injiniyan da ya san aikin sa kadai za a nada wannan mukami.
Sun kuma ce Akpabio ya yi azarbabin nada Manajan Darakta mai riko, Dakta John Nunieh, Alhali Shugaba da mambobin Hukumar Gudanarwar NDDC na gaban Majalisar Datttawa ba a kammala tantance su ba.
Sun ce dama can Akpabio bai cancanci a ba shi minista ba.
Kakakin Yada Labarai na Minista Akpabio ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a dan ba shi lokaci kafin ya ce wani abu.
Akpabio dai ya yi shugabancin jihar Akwa Ibom tsawon shekaru takwas a matsayin gwamna, a karkashin PDP.
Ya fita daga PDP ya koma APC, bayan da EFCC ta zarge shi da karkatar da kudaden jihar sama da bilyan 100.
Ana sauran watanni uku a fara zaben 2019 ya koma APC. Ya tsaya takarar sanata, amma bai yi nasara ba. Buhari ya ba shi Ministan Harkokin Yankin Neja Delta.