FALKE KO SHANSHANI? Kwanaki 500 na Buhari a Kasashen Waje daga 2015

0

Tafiye-tafiye daga gari zuwa wani gari, ko kasa zuwa wata kasa kan kasu kashi uku. Wato fatauci, ziyara ko kuma ragaita. Duk yadda za ka fassara tafiye-tafiye, ba za ka iya daga wadannan da’ira guda uku ba.

Ko fatauci, ko ziyara, ko ragaita ko yawon gallafiri, kakkabar-raba, tafiya hutu ko yawon-bude-ido, duk dai ana nan a cikin wadannan da’ira.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa tarihin zama shugaban da ya fi kowa yawo ko tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a cikin shekaru ukun farko na shugabancin sa daga 2015.

Hakan kuwa tun ana yawaba da yi masa jinjinar tunanin idan ya fita zai dawo da tsarabar da yara da manya ya su yi murnar yi masa ‘Oyoyo ga Baba’, har ta kai an fara gajiya da jin labarin cewa zai fice ya bar kasar nan.

Abin ya kai ga har an koma ana yi wa Buhari ba’a, shagube da gwasalewa. Musamman masu adawa sun koma su na cewa abin fa na Buhari ya tashi daga yawon fatauci ko nema, ya koma sagarabtu, gagaramba, fagamniya, zarya. Ta kai ma a yanzu a na yi wa Buhari lakabi da “Shanshani Sarkin Yawo.”

KWANAKI 404 A SHEKARU 3

1 – A shekara ukun sa na farkon mulki, Buhari ya kwashe kwanaki 404 a kasashen waje. Amma wadannan kwanaki an hada ne har da watannin da ya rika shafewa kwanciya jiyya a London.

2 – A shekaru ukun sa na farko, kenan Buhari ya shafe shekara daya cur har da kwanaki 33 a kasashen 33 da ya ziyarta.

KASASHE 33 CIKIN SHEKARU 3

Kasashen da Buhari ya karade cikin shekaru ukun sa na zangon farko, sun hada da: China, Indiya, Jordan, Iran, Saudi Arabiya da Afrika ta Kudu.

Sai kuma Chadi, Faransa, Turkiyya, Poland, Hadaddiyar Daukar Larabawa (UAE), Morocco da kuma Ghana.

Buhari duk a cikin shekaru ukun farko ya rankaya kasashen Kamaru, Gambiya, Nijar, Mali, Qatar, Sudan, Ivory Coast da Jamus.

Haka kuma Buhari ya lula Sanagal, Ethiopia, Egypt, Kenya, Ka kuma a manta Buhari ya je kasar Amurka sau hudu Taron Majalisar Dinkin Duniya na 70, 71, 72 da na 72 a birnin New York.

Baya ga zaman jiyya da Buhari ya rika yi a London, ya sake shafe jimillar wasu kwanaki 41 a can, sannan kuma wannan tafiya da ya zarce daga Saudiyya zuwa London, zai kara yin wasu kwanaki 14 a birnin.

A shekara ta hudu ta mulkin Buhari bai yi zirga-zirga kasashen waje sosai ba. Kwatsam, cikin daren da aka sake rantsar da shi a karo na biyu, 29 Ga Mayu, 2019, sai dai kawai aka wayi gari da labarin cewa ai ya cira sama ya darzaza kasar Saudiyya.

Dama kuma kwanaki 7 kacal kafin sake rantsar da shi din ya dawo daga Umra a Saudiyya inda ya shafe kwanaki bakwai a can.

Daga sake rantsar da Buhari zuwa watan Oktoba, ya ziyarci Saudiyya har sau biyu, Burkina Fasso, New York, Japan, Afrika ta Kudu da kuma Rasha.

Buhari ya na wadannan tafiye-tafiye ne a lokacin da shi da kan sa me korafin cewa babu wadatattun kudaden shiga a hannu ko asusun gwamnatin tarayya.

Ya bai wa ‘yan Najeriya mamaki ganin yadda ya rubanya kasafin kudin zirga-zirgar da shi da mataimakin sa Yemi Osinbajo za su yi a 2020.

Bayan kuma ya gindaya umarnin hana ministoci da manyan jami’an gwamnati fita kasashen waje ba tare da sahihin dalili ba. Ko da daliki, sai gwamnati ta amince. Idan ta amince kuwa, ta rage kudaden guziri da yawan tawagar da za su rika fita. Duk dai saboda a yi tattalin kudaden gwamnati.

A yau dai Buhari ya yi kwanan London, inda zai shafe makonni biyu kafin ya dawo Najeriya.

Abin da ya fi damun ‘yan Najeriya shi ne, yadda Buhari bai damu da yawan kai ziyara jihohin kasar nan ba, ko da kuwa wani bala’i ko ibtila’i ya afku. Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta fitar da sanarwar jaje, jimami, alhini ko damuwar Shugaba Buhari kawai.

Ba ya zuwa jajen afkuwar mummunar gobara a kasuwanni, ba ya tafiya jajen mummunan harin Boko Haram ko ‘yan bindiga. Amma Buhari ba ya wuce tayin gayyatar taro kasashen waje, ko da na yini daya ne.

Da yawan ‘yan mazabar sa, wato ‘yan Arewa na ganin cewa su dai har yanzu ba su ga an zo musu da wata tsaraba daga waje ba. Watakila shi ya sa suka gaji da yi masa ‘oyoyo ga Baba ya dawo.’

Share.

game da Author