Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin kara jawo mata a cikin harkokin noma ta yadda za su rika samun tallafi da karfi daidai da maza.
Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono ne ya bayyyana haka a Abuja, yayin da ya ke jawabi a wurin kaddamar da shirin.
Nanono ya ce manufa da muradin shirin shi ne a bayar da dama daidai ha kowane jinsi na maza da mata domin a bunkasa samar da abinci a cikin kasa.
“Mata su ne kashi 50 bisa 100 na yawan al’ummar duniya. Sannan su ne kashi 70 bisa 100 masu ayyukan noma a yankunan karkara. Kuma su ne kashi 60 bisa 100 na yawan masu ayyukan sussuka da gyaran amfanin gona. Amma duk a haka ba su da tattalin arzikin kayan amfanin gona a hannun su.”
Ya ce kayan amfanin gona da mata ke mallaka bai fi kashi 20 bisa 100 ba. Wannan kuwa a cewar Nanono, ba karamar matsala da ci baya ba ce.
Sannan kuma ya koka dangane da karanci ilmin mata da kuma rashin yawaitar mata a fannonin bincike.
A na sa bayanin, Shugaban Kwamitin Ayyukan Noma a Majalisar Dattawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga mata da su tashi tsaye, su daina nuna kasala ko jan-kafa, su rungumi fannonon npma don a rika damawa da su.
Mata da yawa sun suna bukatar shiga fannin noma a na gogawa da su, amma sun yi kira ga gwamnati ta rika saurin aiwatar da shirye-shiryen ta, ba sai a rika raratu ko rubuce-ribuce kawai a kan takardu ba.