TARON KIWON LAFIYA: Za a bude asusu domin kula da masu fama da cutar daji a Najeriya – Minista Ehanire

0

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta bude wani asusu domin kula da masu fama da cutar daji a kasar nan.

Ya fadi haka ne a taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya a Najeriya da ake yi a Otel din ‘Nicon Luxury’ dake Abuja.

PREMIUM TIMES, PTCIJ, cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka hada wannan taro mai taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a ji za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan da samar da hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin farashi mai sauki na daga cikin batutuwan da ake tattauna a taron.

Ehanire ya kara da cewa gwamnati za ta kafa wannan asusu ne don taimakawa masu fama da cutar a Najeriya bayan kokawar da wata mata mai suna Serah Shimenenge dake dauke da cutar ta yi kan kaluballen da ta ke fama da su.

Serah ta ce masu fama da wannan cuta a kasar nan na matukar shan tsadar magani, kama gada yin gwaji da kuma siyan magungunan da ya kamata su rika sha akai-akai.

“Muna kokarin ganin cewa asibitoci masu zaman kansu sun bude wani bangare domin kula da mutanen dake dauke da wannan cuta kyauta.

Daga nan Ehanire ya yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin dake haddasa wannan cuta cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

“Wadannan hanyoyi sun hada da guje wa shan giya, shan taba sannan da shakar hayakin sigari.

Ya kuma ce gwamnati ta dauki wasu matakan da za su taimaka wajen wayar da kan mutane game da cutar domin rage yawan mace-macen mutane a kasar nan.

Idan ba a manta ba a watan Fabrairu ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta rawaito cewa mutane 116,000 na dauke da wannan cutar wanda daga ciki mutane 41,000 suka rasu.

Kungiyar ta ce a yanzu haka daji na daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a Najeriya da duniya gaba daya.

Bincike ya nuna cewa karancin ma’aikata, tsadan farashin magani da gwaji na cikin matsalolin da masu dauke da wannan cuta ke mutuwa a Najeriya.

Duk da haka gwamnati ta yi iya kokarinta domin ganin tra samar wa manya-manyan asibitocin gwamnati na’urorin gwaji na zamani.

A yanzu haka Najeriya na da na’urorin gwajin ciwon daji guda takwas a asibitoci daban daban a kasan.

Share.

game da Author