Taron a-yi-ta-ta-karen da aka gudanar jiya Talata tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ya kasa samar da matsaya daya. Wannan ya sa tilas aka dage taron zuwa yau Laraba.
Zai iya yiwuwa cewa amincewar da bangarorin biyu suka yin a su ci gaba da taron a yau Laraba, ya na nufin watakila NLC ba za ta umarci ma’aikata su rangada yajin aikin game-garin da suka yi niyyar yi.
NLC ta yi kurarin tafiya yajin aiki saboda Gwamnatin Tarayya ta tsaya ta na ya yi musu “walle-walle da yawo hankali sama da shekara daya wajen kasa cika alkawarin biyan karin mafi kankantar albashi.”
SABUWAR YARJEJENIYA
Wani babban jami’in da ya halarci zaman tattaunar jiya Talata, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa NLC ta dan sauko kasa, ta rage adadin abin da ta nema a yi wa masu matakin albashi na 07 zuwa 14, daga kashi 29 zuwa kashi 25 na albashin su.
Sannan kuma NLC ta amince tare da rage yawan abin da ta nema a rika biyan masu matakin albashi daga na 15 zuwa na 17, a yi masu karin kashi 20 maimakon kashi 25 da ta nema a yi musu.
Sannan kuma ita gwamnatin tarayya ta nuna alamar yi wa masu mataki na 07 zuwa 09 karin kashi 17, yayin da masu mataki na 10 zuwa na 14 kuma a yi musu karin kashi 15 bisa 100.
Su kuma masu matakin albashi na 15 zuwa na 17, za a yi musu karin kashi 12 bisa 100, kamar yadda majitar ta tabbatar wa wannan jarida.
Yayin da ake sauraren ci gaba da tattaunawar a yau karfe 2:00 na rana, PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda NLC ta yi barazanar tafiya yajin aiki idan har ba a cimma wata matsaya ba.