Shugaban Hukumar Zabe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa idan ana batun sha’anin gudanar da zabe, to jihohin Kogi da Bayelsa na da wahalar sha’ani.
Yakubu ya bayyana haka a jiya Talata, a yayin wani taron neman goyon bayan sarakunan gargajiyar Jihar Bayelsa, wajen tabbatar da ganin cewa an gudanar da zaben gwamnan jihar lami lafiya, a ranar 16 Ga Nuwamba mai zuwa.
Yakuwa wanda kuma ya yi magana da wakilan jam’iyyun da suka fito takara a jihar, ya ce halayyar da manyan ‘yan siyasar jihohin biyu ke nunawa a lokutan zabe abu ne mai kawo wa INEC Kalubale ba karami ba.
Ya ce a yau saura kwanaki 1 a gudanar da zaben gwamna a jihohin biyu. Gaba daya idon duniya duk ya komawa a kan wadannan jihohi biyu, domin ganin yadda INEC za ta gudanar da zabe.
Yakubu ya ce duk an ga yadda aka yi kakudubar gudanar da zabukan fidda-gwani a jihohin biyu, an kuma fara kamfen na neman kuri’un jama’a a ranar zabe, za a ci gaba da kamfen har ana saura sa’o’i 24 a fara zabe. Cewar Yakubu.
Farfesan kuma shugaban na INEC, ya ce za a yi amfani da ma’aikatan INEC 10,000 A Jihar Bayelsa, jihar Kogi kuma 14,000.
Haka nan kuma, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi kakkausan gargadin cewa Dimokradiyya ba kayan sayarwa ba ce. Don haka duk mai kokarin sayen kuri’u a loakcin zaben gwamna, to ya kuka da kan sa.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan dangane da gabatowar zaben gwamna a Jihar Bayelsa.
Yakubu ya yi wannan gargadi a lokacin da ya ke taron ganawa da sarakunan gargajiya na Jihar Bayelsa, inda ya fassara sayen kuri’u tamkar cefanar da dimokradiyyar Najeriya ce a kasuwar ‘yan gwan-gwan.
A taron wanda aka gudanar a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, Yakubu ya ce sayen kuri’u na daya daga cikin kalubalen da INEC ke fama da shi a lokutan zabe a kasar nan.
“ Damuwar mu ta farko ita ce kalaman da ka iya haddasa barkewar rikici a lokutan kamfen, lokutan gudanar da zabe da kuma lokutan da ake tattara sakamakon zabe.
“Wani kalubalen kuwa shi ne saye da sayar da kuri’u. Bai yiwuwa a bar wasu ‘yan gwan-gwan masu kokarin saida dimokradiyya a tsakiyar kasuwa; ya zama tilas a bar kowane dan Najeriya ya zabi wanda ya k era ra’ayi a ranar zabe, ba tare da an cunna masa kudi ya saida ‘yancin sa ba.
“Ya kamata mu tashi tsaye mu dakile annobar sayen kuri’u. INEC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kuma ba ta goyon bayan kowace jam’iyya, ko wani dan takara. Wanda jama’a suka zaba, shi ne zai wakilce su.”
Yakubu ya nuna damuwa dangane da irin yadda jihar Bayelsa ke da wahalar gudanar da zabe, saboda yadda jihar ta ke.
Shi kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Bayelsa, Alfred Diete-Spiff, ya nuna damuwa ganin yadda sojoji ke karaikaina a jihar a duk lokacin da zabe ya zo.
Ya kuma nuna damuwa ganinn yawan masu gudun hijirar da suka rasa muhallin su a wasu sassan jihar ta Bayelsa.
Discussion about this post