Sarakuna na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen samun ci gaba a fannin kiwon lafiya a Najeriya – Sarkin Gombe

0

Mai martaba sarkin Gombe, Abubakar Shehu III ya bayyana cewa idan har ana son samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan sai an yi tsari yadda talaka da mai kudi za su iya samun kiwon lafiya a duk lokacin da suke bukata batare da an fifita wani ba.

“ Tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa ne idan aka kwadaitar da mutane da yin karatun boko. Hakan zai sa su rika gano matsaloli da kan su da kuma yadda za su iya magance su ta hanyar zuwa asibiti da kuma kiyaye wa.

Mai martaba Shehu ya fadi haka ne a taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya a Najeriya da aka yi ranakun Talata da Laraba a Otel din ‘Nicon Luxury’ dake Abuja.

PREMIUM TIMES, PTCIJ, cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka hada wannan taro mai taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a ji za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan da samar da hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin farashi mai sauki na daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron.

Sarki Shehu ya kara da cewa tabbas sarakuna na da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa domin ganin an samu ci gaba a abin da aka sa ka a gaba na ganin fannin kiwon lafiyar kasar nan ya daukaka. Sannan kuma yayi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da su hada hannu da gwamnati wajen ganin manufofi da shirye-shiryen inganta kiwon lafiya ya amfani talakan kasar nan.

Share.

game da Author