A matsayina na dan Kano, gaba da baya, bansan wajen da zanje naci abincin naira talatin ba. Ban kuma ce babu ba, amma inaso a fada min sai na din ga zuwa a matsayina na talaka.
A cikin wannan makon ne, ministan noman Najeriya, Alhaji Sabo Nanono yace babu yunwa a Najeriya kuma ana siyar da abincin naira talatin a Kano.
Gaskiya inaga dai ministan noma tuntuben harshe ya samu, inaga yana so ne yace dari uku (300) ne, saboda nayi imani duk mutumin da yake rayuwa a Najeriya zai yi inkari da wannan maganar. Awara guda uku ce naira talatin, ko magen gidana ba zata kosar da ita ba.

Akwai karancin wadataccen abinci a garin tunda gidaje da yawa sun hakura da cin abinci sau uku a rana. Talakawa sun samu kansu a yanayin da basa iya dafa abinci sau 3 a rana saidai ayi tazarce saboda rashin wadatar abinci.
A zance na gaskiya idan har ana samun haka a garin Kano, me ake tunani a jihar Jigawa, Bauchi, Akwa Ibom, Ebony, Zamfara da Ondo? Matsalar itace, sai an yadda akwai matsala, sannan za a iya maganinta.
Duk girman arziki irin na Kano amma karancin abinci yasa mutane suna dauko mai siyar da abinci suna kawoshi wajen mutane suna magiyar a siya musu saboda abincin shine matsalarsu.
A zahiri ana cikin halin da mutane suke bukatar taimako domin ana jin jiki, ma’aikaci yana kuka, dan kasuwa yana kuka, balle kuma lebura mai neman aikin karfi.
A binciken da Oxfam tayi kwanannan ya nuna cewa mutane miliyan casa’in da hudu da digo biyar (94.5m) ne suke cikin yunwa da fatara a Najeriya.
A satin da ya shige ne, ministan kwadago, Chris Ngege yace mutane miliyan sha biyar (15m) ne suke neman aiki a Najeriya. Wannan maganar yayi ta ne a jihar Anambra.
Tabbas har yanzu akwai yunwa a kasar Najeriya, saidai mun yabawa gwamnati a wasu bangarori da muka ga tana yaki da talauci ka’in-da-na’in, bangarorin sune “Social Investments Programmes”
Cigaba da irin wadannan abubuwan ne zai kawo raguwar fatara da yunwa a Najeriya, tunda mun ga yadda shirin Npower da Cash transfer suke yaki da talauci karara.
Idan matsala ta bujuro, ba a yin musu akan kasancewarta ko rashin kasancewarta, ana tsayawa ne a fitar da hanyoyin yaki da ita. Duk da, a fahimtata, nagane ‘yan Najeriya sun fi fada da abun arziki.
Wannan yana cikin matsalolin Afrika, rashin yadda da faruwar matsala, hakan ne yake jawowa tayi girman da zata bayar da wahala wajen warwarewa.
Muna bayar da shawara ga gwamnatin Najeriya, akwai bukatar a cigaba yaki da yunwa kamar yadda aka dauko hanya. Sannan su ma talakawa sai sun shiryawa fita daga talauci ta hanyar yin abun da ya dace a lokacin da yakamata.
Allah ya shiryar damu.
Discussion about this post