Hukumar kare hakkin ‘dan Adam ta kasa (NHRC) ta koka kan yadda yi wa mata fyade ke neman zama ruwan dare a jihar Gombe.
Kodinatan hukumar Mohammed Ayuba ya bayyana haka yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Gombe ranar Alhamis.
Ayuba ya ce yawa-yawan yi wa mata fyade a jihar na da nasaba ne da rashin kiyaye dokoki da mutunta al’umma, bin iyaye da tarbiya nagari.
“Sanin kowa ne cewa yi wa mace fyade abune dake matukar cutar da mace. Hakan na iya sa ta samu matsalar tabuwar hankali.
“Lokaci ya yi da za a fito a hada hannu gaba daya domin kau da wannan matsala da ya addabi mutanen jihar.
Ayuba ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gyara wasu sassa na dokar domin samun hanyoyin bayyana kwakwaran hujojjin da zai tabbatar an yi wa mace fyade.
Discussion about this post