Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Gombe ta bayyana cewa ta kama masu safarar miyagun kwayoyi har 15 tsakanin watannin Janairu zuwa Satumba.
Shugaban hukumar Aliyu Adole ya fadi haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Gombe ranar Litini.
Adole yace hukumar ta kama wadannan mutane ne da kilogram 523.174 na miyagun kwayoyi wanda a ciki akwai ganyen wiwi.
“Tun dama can akwai wasu masu safarar miyagun kwayoyi guda 66 da hukumar ta kama wanda a yanzu haka wasu daga cikinsu an gurfanar dasu a gaban babbar kotun jihar sannan saura na jiran kotun ta yanke musu hukunci.
“Daga cikin wadannan mutane 66 da muka kama 16 daga manoman ganyen wiwi.
Adole yace abun takaici ne yadda mutane musamman matsasa suka koma ga noman ganyen wiwi a maimakon kayan abinci.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da malaman adini da su hada hannu da hukumar domin ganin an wayar da kan matasa ilollin dake tattare da yin ta’amali da miyagun kwayoyi.
“Muna kuma kira ga iyayen da ‘ya’yan su suka kangare sannan suna ta’ammali da miyagun kwayoyi da su gaggauta kawo su hukumar domin a duba su.
Idan ba a manta ba a watan yuni NDLEA a jihar Kano ta kama masu siyarwa da shigo da miyagun kwayoyi har su 290.
Wadanda aka kama da miyagun kwayoyi a hannun su hukumar ta gurfanar da su a babbar kotun jihar sannan hukumar ta kai mutane 117 asibiti a dalilin illar da shan kwayoyin suka yi musu.