A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi dogon jawabi, domin tuna Ranar Samun ‘Yancin Najeriya, shekaru 59 da suka gabata.
Sai dai kuma tun ba a je ko’ina ba, da dama na ganin cewa kamata ya yi Buhari ya yi magana a kan halin da yankin Arewa maso Yamma, wato shiyyar sa ke ciki dangane da yawaitar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane. Buhari bai yi wannan magana ba.
Akwai Zamfarawa da Sakkwatawa da Katsinawa sama da 40,000 da yanzu haka ‘yan bindiga suka tilasta yin gudun hijira cikin Jamhuriyar Nijar. Banda kuma dubban wadanda Boko Haram suka kora zuwa Nijar daga Barno da Yobe. Duk wadannan Buhari bai ce komai a kan su ba.
Idan aka koma a cikin jawabin sa, za a iya fahimtar yadda Buhari ya rika bayani ya na ci gaba da dora wasu laifuka a kan gwamnatocin da suka gabata.
1 – DALA BILYAN 42.5 KIMSHE A ASUSUN NAJERIYA:
Buhari ya yi bayanin cewa a yanzu a zamanin sa akwai har Dala Bilyan 42.5 a Asusun Najeriya da ke kasashen Turai.
Sai dai kuma Buhari bai yi wa ‘yan Najeriya bayanin tulin bashin da gwamnatin sa ta ciwo ba. Bashin da ya ciwo cikin shekaru hudu ya nunka wanda ya taras ana bin Najeriya gaba daya.
Buhari ya gaji bashin da bai kai Dala Bilyan 30 na. Amma ya zuwa watan Yuli, 2019, ana bin Najeriya bashin Dala Bilyan 81.27, kwatankwacin naira Tirilyan 24.95.
Daga 2018 zuwa 2018 an ciwo kusan naira Tirilyan 2.66. Dukkan wadannan bayanai Dirakatar Ofishin Kula Da Bilyan Basusssuka, Patience Oniha ce ta yi su.
2 – LAIFIN GWAMNATOCIN BAYA
Shugaba Buhari ya dora wa gwamnatocin baya da suka gabata cewa ba su maida hankali a kan wasu fannonin samun kudin shiga ba, baya ga man fetur.
Sai dai kuma wani abin dubawa shi ne, kokarin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi, a farkon hawan sa, inda ya yi amfani da kyakkyawar diflomasiyya aka yafe wa Najeriya basussukan da ake bin ta. Wadannan bashi kuwa ba Obasanjo din ne ya ciwo su ba, gadon su ya yi daga gwamnatocin baya.
3 – KURAKURAN GWAMNATOCIN BAYA A KAN FETUR
Buhari ya yi bayanin cewa a yanzu gwamnatin sa ta dauki darasi daga kurakuran da gwamnatocin baya suka yi a fannin fetur. Shi ya sa a yanzu gwamnatin ta sa ke ririta abin da ake samu daga fetur.
To sai dai kuma babban kuskuren gwamnatocin baya bai wuce biyan kudin tallafin fetur ba, wato ‘subsidy’. Ita ma gwamnatin Buhari a yanzu ta na biya, kuma ‘yan Najeriya sun fi shan fetur da tsada a gwamnatin sa.
4 – ‘YANCIN FADAR ALBARKACIN BAKI
Buhari ya yi bayanin cewa gwamnatin sa ta bada damar fadar albarkacin baki. Wannan magana kuwa jama’a da dama za su yi watsi da ita, idan aka yi la’akari da yawa-yawan mutanen da ake kamawa a tarayya da jihohi idan furta albarkacin bakin su. Yadda tarayya ta yi kaurin suna, haka jihohi da dama suka yi kaurin suna, musamman su a kan masu sukar gwamnatocin su a soshiyal midiya.
5 – YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA
Buhari ya yi bayanin irin hobbasar da gwamnatin sa ta yi a kan yaki da cin hanci da rashawa. Sai dai kuma wadansu matakai da dama wadanda gwamnatin sa ta rika dauka, sun san tuni jama’a da dama sun rika yi wa yaki da cin hanci da rashawa kallon shirin tatsuniya.
Irin yadda Buhari ya cika gwamnatin sa da rikakkun ‘yan PDP, jam’iyyar da ya rika cewa ta kashe kasa, ya haifar da mamaki sosai a kasar nan. Da yawan su kuma da sauran kashi a gindin su, wanda kotu ba ta gama yi musu wankan tsarki ba.
Yadda kotu ta yi gaggawar wanke Sanata Danjuma Goje, cikin kankanin lokaci, bayan daukar shekaru kusan goma ana shari’a, shi ma jama’a na yi masa kallon ‘shari’a-sabanin-hankali.’
6 – KOKARIN MAIDO WA NAJERIYA DALA MILYAN 300 DAGA KUDIN ABACHA
Cikin bayanin Buhari, ya ce Najeriya da Amurka na tattauna yadda za a maido wa kasar nan da Dala Milyan 300, wadanda Abacha ya sata, ya kimshe. Sai dai kuma a fili ta ke cewa Buhari ba sau daya ba, bayan ya hau mulki ya rika cewa Abacha ba barawo ba ne, bai saci kudin Najeriya ba. Duk kuwa da cewa an maido wa Najeriya makudan kudaden da aka ce Abacha din ne ya sace su.
7 – BUKATAR KARA WA DABEN FANNIN SHARA’A SIMINTI
Buhari ya yi bayani akan fannin shari’a. Amma tuni jama’a da dama musamman masu rajin kare hakkin jama’a da ‘yancin Dimokradiyya na ganin cewa labari ne kawai, idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin sa ke take umarnin kotu. Ko kotu ta ce a saki wanda ke tsare, sai gwamnatin Buhari ta yi biris.
Cikin wadanda wannan biris ta yi wa burki, akwai Ibrahim El-Zakzaky, matar sa Zeenat, Sambo Dasuki da kuma na baya-bayan nan, Omoyele Sowore.
8 – BATUN DAKILE BOKO HARAM
Yayin da Shugaba Buhari ke jawabin cewa an dakile Boko Haram, wani dan Majalisar Tarayya daga Jihar Barno ya ce har yanzu Boko Haram na wandaka da warisa a kananan hukumomi takwas na Jihar Barno.
Sannan kuma kwana daya kafin jawabin Buhari, Hukumar Tsarin Sojojin Kasar nan, sun fitar da sanarwar yin gagarimar addu’o’i daga mabiya addinai, domin yi wa matsalar Boko Haram taron-dangi.
9 – CI GABA A FANNIN NOMA
Jawabin Buhari ya nuna irin ci gaban da aka samu a fannin noma a shekaru hudu da rabi da ya yi a kan mulki. To sai dai kuma ba jama’ar kasa ba kadai, ita gwamnatin na sane da cewa har yanzu ana fama da kuncin talauci da yunwa.
Har yau a kullum matasa ‘yan Arewa sai kwarara suke kudanci da tsakiyar Najeriya su na ayyukan kananan sana’o’in ci da kai da kyar. Dako, wankin takalmi, yankan farce, jari-bola duk matasan Arewa ne, kuma a kullum sai kwarara su ke yi.
10 – TUTIYA DA BUNKASA HANYOYIN SAMUN KUDIN SHIGA
Cikin jawabin Buhari, ya yi tutiya kan yadda gwamnatin sa ta fadada hanyoyin samun kudaden shiga, wato harajin cikin gida, yadda za a rika rage dogaro da fetur kawai.
To wannan ma jama’a na ganin cewa ba a yi kokari fiye da gwamnatin baya ba, idan aka yi la’akari da wata wasikar da aka yi zargin Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gamnatin Tarayya, Abba Kyari ya aika wa Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS), Babatunde Fowler.
Wasikar ta nuna damuwa kan yadda kudaden shigar da ake tarawa ba su ma kai na wasu shekaru a lokacin mulkin Jonathan ba.
11 – SAMAR WA MATASA SAHIHIYAR MADOGARA
Buhari ya ce gwamnatin sa ta Gina matasa ta hanyar samar musu hanyoyin dogaro da kai daga abin bukatun su wajibi. Tuni masu adawa na ganin ai har yau Buhari bai yi irin kokarin da Jonathan ya yi ba, wanda ya gina wa matasa jami’o’in gwamnatin tarayya har guda 14.
BAYAN SHEKARU 59: Jiya Najeriya ta cika shekaru 59 da samun ‘yanci. Sai dai kuma sama da shekaru 15 kenan ba ta da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na ta.
Wadanda suka durkusar da Nagerian Airways na nan ba a hukunta su ba. Duk kuwa da cewa gwamnatin Buhari ta biya tsoffin ma’aikatan kamfanin kudaden albashi da fanshon su na baya da su ke bi.
Sauran shekara daya mu cika shekara 60 da samun ‘yanci. Me za a yi cikin wannan shekara daya, wanda a cikin shekaru 59 ba a yi ba?
Mu na ji, mu na gani, mu na kuma saurare.