‘Yan sanda sun kama tsohon da yayi wa ‘yar shekara 11 fyade

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama wani tsoho mai shekaru 75 da ya yi wa ‘yar shekara 11 fyade.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ebere Amaraizu ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Enugu ranar Talata.

A takardan Amaraizu ya bayyana cewa wannan tsoho na aikin gadi ne a makarantar sakandare dake kauyen Ugbaike a karamar hukumar Igbo Eze sannan ya rika danne wannan yarinya ne a daya daga cikin ajujuwan dake makarantar.

“Rundunar ta samu labarin haka ne daga mutumin da ya kama wannan tsoho turmi da tabarya akan yarinya.

“Bayanai sun nuna cewa tsohon ya Dade Yana yin lalata da dalibai a makarantar.

Ya ce tsohon ya amsa laifinsa sannan ya nemi a yafe Masa cewa hudubar shaidan ya bi.

Rundunar dai na tsare da wannan tsoho sannan za a kai shi kotu bayan sun kammala bincike.

Share.

game da Author