Najeriya ta kama hanyar zama kasa mai jam’iyya daya – APC

0

Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da sanarwar damuwar ta, ganin yadda jam’iyyar adawa ta PDP ba ta yin adawa mai zafi-zafi.

APC ta ce irin yadda PDP ba ta kazar-kazar wajen nuna adawa sosai, abin damuwa ne da ke neman jefa kasar nan zuwa kasa mai jam’iyya daya tilo.

Wannan bayani na APC ya fito duk kuwa da cewa PDP ta samu karfi sosai a zaben 2019, inda ta kafa gwamnati a jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai, Sokoto a Arewacin kasar nan, sannan kuma ta lashe jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da kuma jihar Oyo a yankin Kudu maso Yamma.

Sai dai kuma wannan bai hana APC gwasale PDP ba, inda ta nuna cewa: “Dimokradiyya ba za ta yi armashi ba, a yayin da jam’iyyar adawa (PDP) ba ta da wani kuzarin da ta ke iya yin wani katabus, ta ‘shirim ba ci ba.’’

“Maimakon a ce PDP ta tashi gadan-gadan ita da ‘yan kazagin ta su na adawa mai ma’ana, sai su ka buge da irin tatsuniyar su ta surutan karyar ikirarin cin zabe, kirkirar karairayi, kucurkuda tuggun karya don haifar da sabani a cikin gwamnati, sai kuma ragon tunanin su da su ka gaskata tasuniyar wai Jubril daga Sudan ne ke shugabancin kasar nan.”

“A yayin da wannan gwamnati ke fuskantar kalubale, kuma a wannan lokacin da duk mu ka maida kai wajen ayyukan gina kasa, abin da kawai ita kuma PDP ta fi maida hankali a kai, shi ne karkatar hankulan jama’a.

Yayin da PDP ke ta yi wa kan ta tsirara a tsakiyar kasuwa, ita kuwa APC za ta ci gaba da kara maida hankali wajen ayyukan ci gaban kasar nan.

APC ta kara yin tuni da cewa kada jama’a su manta irin halin da jam’iyyar ta samu kasar nan a lokacin da ta karbi mulki a hannun PDP.

Sanarwar wadda kakakin yada labarai na APC Malam Issa ya sa wa hannu, ya ce APC ta yi rawar gani, musamman yadda ta ceto kasar nan daga matsin tattalin arziki, wanda aka shiga, bayan da mulkin PDP ya yi wa tattalin arzikin kasar nan raga-raga.

Share.

game da Author