Buhari ya roki Majalisa ta amince wa Kogi karbar naira biliyan 10

0

Wata daya cur kafin zaben gwamna a jihar Kogi, Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wa Majalisar Dattawa takardar rokon ta amince a bai wa Jihar Kogi naira bilyan 10, ramuwar kudaden da ta yi wasu ayyuka a jihar, wadanda gwamnatin tarayya ce ya kamata a ce ta yi su.

Wannan roko ya na cikin wasikar da Buhari ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, kuma ya karanta ta yau Talata a zauren Majalisar Dattawa.

Wannan biyan kudi, ba tsabar zunzurutun kudi ba ne ake bayarwa, takardar alkawarin za a biya kudi ce, wato ‘promisory note’, a wani lokaci, ko rana a kan wasu sharudda.

Sai dai kuma mutum zai iya amfani da wannan takarda a banki ya karbi wasu kudade, ganin cewa akwai wasu kudi na sa da aka yi masa alkawarin za a ba shi nan gaba, kamar yadda takardar alkawarin ta nuna.

Da ya ke karanta wasikar, Lawan ya ce Majalisar Dattawa Zango na 8 da ta gabata, sun amince da a bai wa jihohi 24 daga cikin 25 irin wannan takardar alkawarin biyan kudi.

A cikin wasikar, Buhari yace Gwamnatin Tarayya ta bincika, kuma ta gamsu cewa dukkan jihohin 25 sun yi ayyukan da suka yi ikirarin cewa sun yi a madadin gwamnatin tarayya.

Ya ce Majalisar Zartaswa ta amince da biyan kudin da kuma gamsuwa da ayyukan da suka ce sun yi.

Daga nan sai Sanata Lawan ya umarci Kwamitin Majalisar Dattawa a kan Basussukan da aka ciwo Kasashen Waje da cewa su bi diddigin wannan takardar roko da Buhari ya aiko, kuma su kai wa Majalisa rahoto nan da makonni biyu.

Share.

game da Author