TARON KIWON LAFIYA: Idan iyaye suka san hakkokin ‘ya’yan su a kan su zai rage matsaloli da dama – Oloyode

0

Rajistaran hukumar shiya jarabawar shiga jami’o’I ta kasa (JAMB) Ishaq Oloyede ya bayyana cewa wayar da kan iyaye game da sanin hakokkin dake rataye a kafadun su game da ‘ya’yan su musammamn wadanda suka shafi kiwon lafiya zai taimaka matuka wajen rage matsalolin da fannin ke fama da shi a kasarnan.

Oloyede ya fadi haka ne a taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya a Najeriya da ake yi a Otel din ‘Nicon Luxury’ dake Abuja.

PREMIUM TIMES, PTCIJ, cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka hada wannan taro mai taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a ji za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan da samar da hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin farashi mai sauki na daga cikin batutuwan da ake tattauna a taron.

Oloyede ya ce wayar wa da iyaye kai game da yadda za su rika kula da ‘ya’yan su musamman ta hanyar shawarwari ga ‘ya’yan su mata da kuma sa musu ido wajen kiwon lafiyar su zai taimaka matuka.

“Tabas yin haka zai taimaka wajen ganin ‘ya’yan mu mata sun samu ilimin boko, ingantaccen kiwon lafiya da sauran su.

Ya ce duk haka zai yiwu ne idan malaman addini sun taimaka wajen wayar da kan mutane game da mahimmancin samar wa ‘ya’yan su kiwon lafiya na gari.

“ Haka ya nuna cewa malaman addini na da muhimmiyar rawan da za su iya takawa don ganin haka ya tabbata. A dalilin haka yake kira ga malaman addini da su rika fitow asu na gyara tarbiyar ya’ya ta hanyar kwaban su da sanar da su amfanin yin haka.

Ya ce akwai camfe-camfe da ake yi musamman a karkara kan wasu cututtuka da mai makon a garzaya asibiti cikin gaggawa sai kaga ana jingina shi da addini ko kuma al’ada. Ya ce dole sai malamai sun rika fadakar da al’umma akai akai.

Share.

game da Author