KURUNKUS: Buhari ba zai yi takara a 2023

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen cece-kucen da ake ta yi a shafunan soshiyal midiya cewa wai yana shirin canja kundin tsarin mulkin Najeriya domin samu damar sake tsaya takara a 2023.

Kakakin fadar gwamnati, Garba Shehu ne ya bayyana haka a takarda da ya fitar da ga fadar gwamnati ranar Takara.

Shehu ya ce babu wannan magana Kuma ma dai Buhari ba irin wadancan bane.

” Shugaba Buhari zai kammala wa’adin sa na biyu sannan ya tattara nasa-ina-sa ya fice daga gidan gwamnati. Za a yi zabe a wannan lokaci Kuma shi ba zai Yi takara ba.

” Buhari mai bin doka ne sau da kafa, ba zai taba yin wani abu da zai kawo rudani a kasa ba. Idan wa’adin mulkinsa ya cika, zai tafi.

Idan ma wani ya nemi yin wani abu kamar haka, ba zai samu goyon bayan shugaban Buhari ba.

” A da an samu labarin Wasu sun so su Yi haka amma abin bai yiwu ba. Buhari ba zai taba yin abin da ba haka yake a doka ba.

Share.

game da Author