Shugaban karamar hukumar Keffi a jihar Nassarawa Abdulrahaman Maigoro ya biya wa dalibai 500 ‘yan asalin karamar hukumar kudin jarabawar kammala karatun sakandare wato WAEC,NECO,NABTEB da JAMB.
Maigoro ya sanar da haka ne a taron bukin samun ‘yancin kai da aka yi a karamar hukumar ranar Talata.
Ya ce ya yi haka ne don tallafa wa iyayen da basu da karfin iya biya wa ‘ya’yan su kudin jarabawar kammala karantun sakandare din sannan da inganta samun ilimin boko a karamar hukumar da jihar baki daya.
Bayan haka Maigoro ya kuma saka yara 8,000 a makarantun firamare yan asalin karamar hukumar
“Mun tallafa wa yaran da muka zabo daga gidajen da iyayen su basu da karfin samar wa ‘ya’yan su ilimin boko a jihar sannan mun kuma samar wa wadannan yara rigunan makaranta,takardu da dai sauran kayan da za su bukata.
Ya yi kira ga duk yaran da gwamnati ta dauki nauyun su da su maida hankali wajen karatunsu.
A karshe sakataren hukumar kula da ilimi na jihar Emmanuel Barau ya jinjinawa shugaban karamar hukumar bisa namijin kokari da yayi da kuma maida hankali wajen ganin mutanen sa sun samu ilimin Boko a fadin karamar hukuma.
Barau ya yi kira ga sauran wakilan gwamnati da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da suyi koyi da irin abin da Maigoro yayi.