Tsarin karba-karba zai iya zame wa zaben 2023 alakakai – Jami’ar Amurka

0

Jami’ar diflomasiyyar Amurka, mai suna Linda Thomas-Greenfield, ta bayyana cewa tsarin yarjejeniyar karba-karbar mulkin Najeriya zai iya zama alakakai ga zaben 2023.

Ta bayyana haka a lokacin da ta ke jawabi a taron kwanaki biyu na cikar dimokradiyyar Najeriya shekaru 20 da kafuwa daram.

An gudanar da bikin a Washington DC, Amurka, inda Linda ta ce siyasa a Najeriya ta zama kawai wata kungiyar dattawa, kamar yadda jaridar Cable ta ruwaito ta na bayyanawa.

Kungiyoyin rajin kare dimokradiyya uku, wato NED, Ford Foundation da kuma YIAGA Africa ne su ka hada guiwar shirya taron.

“Siyasar Najeriya dai ta zama wani kulob wanda dattawa ne akasarin mambobin ta. Sannan akwai babban kalubalen yarjejeniyar maida mulki zuwa yankin kudancinn kasar, a bisa tsarin karba-karba. Dalili kenan wannan zabe mai zuwa na 2023 zai fuskanci kalubale.” Inji Linda.

Duk da cewa tsarin mulkin kasar nan bai bayar da wata kofar tsarin karba-karba ba, wasu na ganin karba-karba wata maslaha ce da ke tattabar da adalci da raba-daidai din mulki da mukamai ga yanki ko wata kabila.

Shekara 20 kenan ana yin karba-karba din mulkin shugaban kasa a fannin siyasa, tun bayan dawowa mulkin farar hula cikin 1999.

Buhari dan Arewa ya gaji Jonathan daga kudancin kasar nan. Shi kuma Jonathan ya gaji dan Arewa Umaru Yar’Adua, wanda shi kuma ya gaji Olusegun Obasanjo, dan Kudu.

Idan ba a manta ba, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya yi kiran da a soke tsarin shugabancin karba-karba.

Ya ce kamata ya yi a rika zaben shugabanni a bisa cancantar su kawai ba wai a mika mulki ga wanda bai cancanta ba, saboda dalilai na kabilanci a cikin siyasa.

Share.

game da Author