Gwamnatin jihar Bauchi ta kori wani shugaban makarantar kwana a Hassan Usman Katsina Unity Collage (GHUKUC) a dalilin kin ciyar da yaran makarantan abinci yadda ya kamata.
Kwamishinan ilimi na jihar Aliyu Tilde ya sanar da haka a wani takarda da ya aika wa PREMIUM TIMES ranar Alhamis.
Tilde yace binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa masu girkawa daliban abinci na ciyar da dalibai 350 daga cikin 1,200 din da ya kamata a makarantan kawai.
Ya ce hakan na faruwa ne a wannan makaranta bayan gwamnati ta tanadi isassun kayan abinci wa duk makarantun kwanan dake jihar kafin dalibai su dawo hutu.
Tilde yace a dalilin haka kuwa gwamnati ta kori shugaban makarantar sannan har an maye gurbin sa da wani.
“Nan ba da dadewa ba za a saka jami’an tsaro a duk makarantun kwana dake jihar domin hana maimaicin irin haka a nan gaba.
Bayan haka gwamnan jihar Bala Mohamme yace gwamnati ta dauki matakan da za su taimaka wajen ganin yara sun samu ingantaccen ilimin boko jihar ganin cewa bincike ya nuna adadin yawan yaran dake gararamba a jihar ya fi na kowacce jiha yawa a arewacin Najeriya.
Ya ce hakan zai yiwu ne idan aka inganta shirin ciyar da dalibai abinci da zai kaifafa kwakwalwar su.
Idan ba a manta ba rahotanin sun nuna cewa shirin ciyar da daliban makaranta abinci miliyan 9.8 a jihohi 32 a kasar nan.
A yanzu haka gwamnati na ciyar da daliban makarantun firamare 53,000 tare da daukan masu girka abinci 106,000 a jihohi 32 dake kasar nan.
Gwamnati ta tsara haka ne domin kawar da yunwa a yara da hana yawan gararamban da yaran da basu zuwa makaranta a kasar nan ke yi.
Sai dai duk da haka wannan shiri na fama da wasu matsaloli da suka hada da yin sama da fadi da kudaden da ake ware wa domin ciyar da daliban, yin watanda da kayan abincin,rashin ciyar da yara abinci mai inganci da yawan da ya kamata, rashin daukan isassun ma’aikata da dai sauran su.