KARIN ALBASHI: An daura aure da marar kwabo

0

Bayan shafe kwanaki ana tirka-tirkar tattauna neman cimma matsaya a kan batun karin albashi, a karshe dai Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago sun cimma yarjeniyar tsara karin albashi mafi kankanta, tun daga kan mai matakin albashi na 07 har zuwa na 17.

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta rigaya ta amince da karinn kashi 30 bisa 100 ga kananan ma’aikata masu matakin albashi daga 01 zuwa 07.

An cimma wannan yarjejeniya ce bayan an shafe dogon lokaci ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tun daga karfe 8:24 na dare har zuwa karfe uku na asubahin yau Juma’a.

Ministan Harkokin Kwadago, Chris Ngige ne ya bayyana cimma yarjejeniyar a yau Juma’a bayan sun tashi daga taron.

YARJEJENIYAR DA AKA KULLA

Ga abin da yarjejeniyar ta kunsa a takaice, kamar yadda Minista Ngige ya bayyana wa manema labarai bayan tashi daga taron:

KARIN DA AKA YI RUKUNI NA 1 (CONPSS)

• GL 07 = 23.2%
• GL 08 = 20%
• GL 09 = 19%
• GL 10 – 14 = 16%
• GL 15¬ 17 = 14%

KARIN DA AKA YI WA RUKUNI NA 2 (CONHESS, CONRAISS, CONTISS II, CONUASS II, CONMESS. CONTEDISS & CONPCASS)

• GL 7 = 23.2%
• GL 8-14 = 16%
• GL 15-17 = 10.5%

An sha zaman neman cimma yarjejeniya daya a baya, amma abin bai yiwu ba. Taron a-yi-ta-ta-karen da aka gudanar ranar Talata tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ya kasa samar da matsaya daya. Wannan ya sa tilas aka dage taron zuwa ranar Laraba.

Zai iya yiwuwa cewa amincewar da bangarorin biyu suka yin a su ci gaba da taron a yau Laraba, ya na nufin watakila NLC ba za ta umarci ma’aikata su rangada yajin aikin game-garin da suka yi niyyar yi.

NLC ta yi kurarin tafiya yajin aiki saboda Gwamnatin Tarayya ta tsaya ta na ya yi musu “walle-walle da yawo hankali sama da shekara daya wajen kasa cika alkawarin biyan karin mafi kankantar albashi.”

Wani babban jami’in da ya halarci zaman tattaunar jiya Talata, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa NLC ta dan sauko kasa, ta rage adadin abin da ta nema a yi wa masu matakin albashi na 07 zuwa 14, daga kashi 29 zuwa kashi 25 na albashin su.

Sannan kuma NLC ta amince tare da rage yawan abin da ta nema a rika biyan masu matakin albashi daga na 15 zuwa na 17, a yi masu karin kashi 20 maimakon kashi 25 da ta nema a yi musu.

Sannan kuma ita gwamnatin tarayya ta nuna alamar yi wa masu mataki na 07 zuwa 09 karin kashi 17, yayin da masu mataki na 10 zuwa na 14 kuma a yi musu karin kashi 15 bisa 100.

Su kuma masu matakin albashi na 15 zuwa na 17, za a yi musu karin kashi 12 bisa 100, kamar yadda majitar ta tabbatar wa wannan jarida.
Yayin da ake sauraren ci gaba da tattaunawar a yau karfe 2:00 na rana, PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda NLC ta yi barazanar tafiya yajin aiki idan har ba a cimma wata matsaya ba.

Sai dai kuma wannan duk ya wuce, ganin cewa an amince da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma a yau Juma’a da asubahi.
Yanzu ya rage ga gwamnati ta shirya lokacin da za ta fara aiwatar da karin baki daya.

Daga nan kuma sai a ga abin da zai wakana a sauran jihohin kasar nan, musamman wadanda suka ce sai gwamnatin tarayya ta fara biyan karin albashin sannan za su fara su ma.

A na ta bangaren, a baya gwamnatin Buhari ta ce babu kudin da za a yi karin albashi har sai an nemo karin hanyoyin kudaden shiga.

Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta bijiro da hanyoyin karin haraji birjik, domin a samu kudaden shigar da za a rika biyan ma’aikata albashi.

Cikin irin harajin da aka kara, har da na jiki-magayi, wato ‘VAT’, wanda a kokaci daya aka kara kashi 50 bisa 100 na jimillar kudin ‘VAT’ din. Wato daga 5 bisa 100 zuwa 7.5 bisa 100.

Wannan kari da aka yi bakatatan kuwa ya janyo ce-ce-ku-ce da gunaguni a kasar nan, musamman tunanin cewa gwamnatin Buhari ta hau mulki dauke da tulin alkawurran samar wa ‘yan Najeriya rahusar kuncin rayuwa.

A maimakon haka, sai kara lafta musu dakon kuncin rayuwar ake yi, kamar yadda wasu da dama ke ta sharhin su kan tsare-tsaren da Shugaba Buhari ke bijiro da su da sunan neman kudin shiga aljihun gwamnati mai zurfin rami gaba dubu, mai wuyar cikewa.

Share.

game da Author