Za a kwaso ‘yan Najeriya 320 daga Afrika Ta Kudu ranar Laraba – Jakada

0

Jakadan Najeriya da ke Afrika ta Kudu, Godwin Adama, ya bayyana cewa tawagar farko ta ‘yan Najeriya 320 za su baro kasar Afrika ta Kudu zuwa Legas, Najeriya.

Adama ya shaida wa manema labarai cewa ana sa ran za su baro baro Afrika ta Kudu karfe 9 na safiyar gobe Laraba.

Ya ce kamfanin sufurin jirage na Air Peace ne zai yi jigilar dawo da su Najeriya, su sama da 600 da suka nuna bukatar dawowa gida Najeriya.

Ya ce ragowar 320 kuma za su dira Najeriya a jibi Alhamis.

Ni Zan Dawo Da su Najeriya Kyauta

Cikin makon da ya gabata ne dai Shugaban Kamfanin Jiragen Air Peace, Allen Onyema ya dauki nauyin tura jirgin sa domin kwaso ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu masu son dawowa gida.

Ya ce kuma kyauta zai dauko su, ba tare da biyan ko kwandala ba.

Ya kuma gargadi masu dawowar da kada su sake a damfare su a ce su biya kudin dawo da su ko wasu kudaden da babu gaira babu dalili, domin kyauta kyauta zai maido su gida.

Ya ce su yi kaffa-kaffa da wasu masu kokarin damfarar su wai su biya dala 1000. Domin a cewar sa, babu wanda za a karbi ko sisi daga gare shi.

Idan ba a manta ba mataimakiyar Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana wa manema labarai cewa akwai masu son dawowa Najeriya har su 649 daga Afrika ta Kudu.

Ta yi wa Kwamitin Majalisar Dattawa wannan bayani ne a lokacin da ta masar gayyatar jin bin ba’asi daga kwmitin kula da mazauna kasashen waje, a jiya Litinin.

Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki kadan bayan da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya yi irin wannan ganawa da wannan kwamiti.

Sannan kuma idan za a tuna tun a makon da ya gabata ne jirgin Kamfanin Peace Air, ya yi balantiyar dawo da masu son dawowa, duk da dai an samu tsaiko saboda rashin ingantattun takardun fasfo na wasu maso son dawowar.

Share.

game da Author