Zan maida hankali wajen inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan – Minista Ehanire

0

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa zai maida hankali wajen ganin gwamnati ta fara aiki da dokar kiwon lafiya na shekarar 2014 da aka gyara a kasar nan.

Ehanire ya fadi haka ne da yake tattaunawa da kwamitocin kiwon lafiya na majalisar dokoki ta kasa a taron da aka yi a Abuja a makon da ya gabata.

Ya ce tun 1999 zuwa yanzu fannin kiwon lafiyar kasarnan bata iya tabuka wani abin azo a gani ba na inganta kiwon lafiyar mutanen Najeriya.

Ehanire yace haka na da nasaba ne da rashin amfani da dokokin inganta fannin, rashin yin amfani da kudirori da shiriye-shiryen da za su taimaka wajen samar da ci gaba a fannin.

“ Barin baku misali gwamnati ta kirkiro tsarin shirin inshoran kiwon lafiya a 1962. Wannan tsari bai fara aiki ba sai a 2005. Kuma ko a lokacin da aka fara wannan tsari mutane kalilan ne suka samu daman shiga shirin. Yanzu dai idan aka kara gyara tsarin sannan mutane suka samu daman shiga shirin lallai za a samu ci gaba matuka fiya da yadda ake tsammani.

Dokar kiwon lafiya na 2014

A bincike da PREMIUM TIMES ta yi game da wannan doka ta gano sassa da dama a dokar da har yanzu gwamnati bata fara amfani da su ba.

Daga cikin wadannan sassa kuwa akwai sashen da dole duk wani babban asibiti dake aiki a kasarnan sai ya karbi lasisin amincewa ya gudanar da aiki a kasar bayan an tabbatar da ingancin sa

A karshe ya yi kira ga majalisar dokoki ta kasa da su taimaka wajen ganin kudaden da gwamnati ta ware wa fannin kiwon lafiya a kasafin kudin kasa.

Share.

game da Author