Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Bauchi (BSHCDA) ta bayyana cewa gwamnati za ta yi feshin magani a dajin Yankari domin hana yaduwar cutar Shawara da sauran cututtuka.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da jirgin sama wajen yin wannan feshin magani don kashe kwarin dake baza wannan cuta.
Shugaban hukumar Rilwanu Mohammed ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Bauchi.
Mohammed yace za a yi feshin ne da sassafe saboda a wannan lokaci ne suka fi fitowa.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne daliban kwalejin koyar da malunta dake Waka-Biu a karamar hukumar Biu, jihar Barno suka kamu wasu irin cutuka bayan sun ziyarci Yankari din.
Rahotanin sun nuna cewa dalibai hudu sun rasu sannan 12 na kwance a asibiti.
Bayan kwanaki biyu hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta tabbatar cewa zazzabi shawara ya bullo a jihar.
Daga nan kuma a ranar 9 ga watan Satumba hukumar ta gwada jinin mutane 34 daga kananan hukumomin Bauchi,Tafawa Balewa, Dass, Ganjuwa da Alkaleri inda aka gano cutar a jikin wasu, sannan wasu ma sun rasu.
Mohammed yace a dalilin wannan sakamako gwamnati ta ware magungunan allurar rigakafin cutar guda 600,000 domin yi wa mazauna karamar hukumar Alkaleri rigakafi.
Ya kuma ce gwamnati za ta raba gidajen sauro da yin feshi a dakunan ma’aikatan daji.
“Mun gano cewa mafi yawan mutanen da suka rasu a dalilin kamuwa da cutar ma’aikatan wannan daji ne.
Mohammed ya ce gwamnati ta yi wa masu yi wa kasa hidima 1,700 a sansanin ‘yan bautan kasa a jihar allurar rigakafi.
A karshe gwamnati zata yi wa duk wanda zai shiga dajin Yankari allurar rigakafi domin kariya da kuma hana yaduwar cutar.