‘Yar sanda ta zargi mijin ta da kokarin yin kudin tsafi da ita

0

Wata ‘yar sanda mai mukamin saje, mai suna Wulaola Babalola, ta shigar da karar mijin ta a Kotun Gargajiya ta Ibadan, inda ta nemi a raba auren su, bisa zargin mijin ta ya yi kokarin yin tsafi da ita domin ya samu tsabar kudi.

Ta nemi a raba auren ta da mijin ta mai suna Oladimeji da suka shafe shekaru 14 a zaman miji da mata tare.

Ta shaida wackotun cewa mijin na ta ya yi amfani da kayan tsafi da surkulle iri daban-daban a duk lokacin da zai neme ta su kwanta tare.

Wuraola ta kara da cewa ya maida ta wata jaka, wadda ya ke yawan jibgar ta.

“Abu kadan sai duka, sai kuma ya tube ni zigidir, ya hana dangi na gani na.

“Ya kan sa min wasu surkulle da tsatsube-tsatsube cikin al’aura ta a duk lokacin da zai kwanta da ni. Sannan kuma ya na kewayen kwanon abinci na da wasu layu da karhuna, wai da nufin ya na kare ni daga miyagun mutane.

“Baya ga wannan kuma ya bi duk a cikin gidan mu ya tona ramu ya rufe layu da guraye tare da ambaton suna na a duk ramin da zai rufe gurayen. Babban da na ya ga lokacin da ya ke haka din.

“Ina da shaidar dukkan layu da gurayen da ya rufe da kuma irin yadda ya ke lakada min dukan tsiya. Da yadda ya ke ci min mutunci a waya idan ya kira ni.” Duk inji matar, wadda sajen ce ta ‘yan sanda.

Sai dai kuma lokacin da ake wannan shigar da kara, mijin ba ya nan ballantana ya amsa zargin da ake yi masa.

Magatakardar kotu ya shaida cewa ya sha kai wa wanda ake karar sammacen kotu. Ya kara da cewa a rukunin gidajen Oluyole Estate ya ke zaune, a Ibadan.

Bayan da Shugaban Kotun, Ademola Odunade ya gama sauraren korafin matar, nan take ya raba auren a bisa dalilin barazanar kisa da ya ce mijin na yi wa matar.

Daga nan kuma mai shari’a ya yanke hukuncin cewa matar ce za ta ci gaba da rike ‘ya’yan su uku. Sannan ya ce a tabbatar mijin ya rika biyan ta naira 15,000 kudin ciyar da ‘ya’yan a kowane wata.

Daga nan ya umarci cewa a tabbatar an aika wa mijin da kwafen takardar hukuncin da kotu ta yanke.

Share.

game da Author