Wata kungiya ta matasan sufaye ta yi Allah wadai da harin da magoya bayan kungiyar Kwankwasiyya ta siyasa ta kaiwa ministan sadarwa kuma malaman addini, Sheikh Isa Ali Pantami.
Kungiyar mai suna (Sufi Youth Movement of Nigeria) a wata sanarwa da shugabanta na kasa Ustaz Sham’un Musa Gabari da sakatarenta Muslihu Yusuf Ali ta ce tilas a nemi afuwar malamin.
An samu bullar wani faifan bidiyo na magoya bayan Kwankwasiyya inda suka yiwa Sheikh Pantami ihun ature a filin jirgin sama na Kano a ranar Talata da ta wuce.
Ministan na hanyarsa ta komawa Abuja ne bayan ya gabar da ta’aziyyarsa ga Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, shugaban kwamitin majalisar tarayya kan sha’anin tsaro bisa rashin mahaifinsa da ya yi a Sharada a cikin birnin Kano.
“Sannan kuma muna kira da babbar murya ga su jagororin wannan kungiya da su gaggauta ba da hakuri a kan abinda ya faru.”
Kungiyar kuma ta yi kira ga duk al’ummar musulmi na kowanne bangare ko akida da su fito su yi tofin Allah tsine kuma su yi Allah wadai ga abinda aka yiwa malamin.
Far wa sheikh Pantami
Tun bayan wannan hari da aka kai wa sheikh Pantami, mutane suka rika fitowa suna tofa albarkacin bakinsu game da wannan mummunar aiki da wadannan matasa suka aikata.
Shi dai Sheikh Pantami bai ce komai ba kuma ma ko a wannan bidiyo da aka rika yadawa an nuno shi ya kutsa cikin matasan cikin fara’a duk da suna yi masa tsangwama yana kokarin gaisawa da su.
Wasu daga cikin dandazon matasan har hotuna suka rika dauka da shehin malamin a lokaci da wasu ke gurza masa rashin mutunci.
An yi kira ga ‘yan siyasa da su rika yi wa mabiyan su fada game da aikata irin wannan abu musamman ga mutane masu daraja irin sheikh Pantami.
Akan samu irin haka sau da yawa idan magoya wani dan siyasa suka gamu da wadanda ba jam’iyyar su daya ba.