Zango ya maida wa malamin da ya ce yana tara mata kanana domin yin fim dasu

0

” Wannan shine Alkur’ani mai girma. Na rantse da Allah, Wallahi Billahi, Wallahi Tallahi, duk abinda ka fada a wannan mumbarin akai na karya kake yi.

” Duka yarinyar da kaga na kawo ta cikin fim ita ta kawo kanta ta ce zata yi fim, ko kuma gani nayi wata ya saka ta nima na dauke ta na saka ta. Idan kuma sabuwa ce, iyayenta suka kawo ta, ko kuma ita ta kawo kanta. Iyayen ta basu yarda in yi kokari in shiga in tabbatar da cewa iyayen ta sun yarda.

” Tun da na fito na yi tallan sabon sarki aka fito ana ta yayada ni cewa wai ina so in lalata mutane.”

Haka dai Adam zango ya rika bayani yana fadin yadda ya shirya duka abubuwansa ba tare da ya saba wa wani shiri ko karantarwar musulunci ba.

Ya yi kira ga malamin da ya garzaya ya nemi wakokin sa domin ya saurara, cewa shi ma yana bada gudunmuwarsa matuka ta hanyar sana’ar sa domin gyara al’umma.

Share.

game da Author