“Wanda ya ce sanatoci ba za su hau motar alfarma ba ya raina mu” – Sanatoci

0

Shugaban Masu Rinjiye a Majalisar Dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ya yi tir da hayaniyar da ake yi dangane da sukar sanatoci don za a sai musu motocin alfarma na naira bilyan 5.550

Ya ce Sanatocin Najeriya sun cancanci hawa motocin alfarma samfurin SUV.

“Ai cin fuska ne ma a rika sukar mu don za a ware kudi a sai mana mota SUV.”

Ya shaida wa ‘yan jarida cewa matsayin sanatocin Najeriya sun fi karfin mota SUV. Haka dai ya bayyana jiya Laraba ga manema labarai.

“Shin wai mene ne wata matsala a nan? A gaskiya cin fuska ne a ce wai sanatan Najeriya ba zai hau ‘Jeep’ ba. Kudin nan fa na Majalisar Dattawa ne, kuma an rigaya an zuba su a cikin kasafin kudi. Sannan kuma ba kyauta ba ne, kowa zai biya idan ya kammala wa’adin san a shekara hudu a majalisa.

“Ni tsohon babban sakatare ne. Na san abin da kowane Minista ke samu. Ba za mu iya ma hada ministoci da mu ba, saboda mun fi minista mukami a kasar nan.

“Amma a haka har ku rika cewa wai sanatan Najeriya ba zai hau ‘Jeep’ ba, wannan ai cin fuska ne ma ake yi mana.

“Ku je ku shaida wa jama’a cewa aikin da mu ke yi ya fi aikin minista nesa ba kusa ba. Nauyin aikin da ke kai na a yanzu haka babu wani minista da ke da irin wannan nauyin aikin a kan sa. Saboda lalacewar tsarin aikin kananan hukumomi, yanzu kusan aikin na su duk ya dawo a wuyan sanatoci.”

Share.

game da Author