Babbar Kotun Tarayya ta kama wasu jami’an kamfanin P&ID, ‘yan Najeriya da laifin harkallar kwangilar da ta haifar da hukuncin biyan diyyar naira tiriliyan 3.2 ga kamfanin na P&ID.
Daga nan sai kotun ta umarci EFCC ta rike dukkan kadarorin P&ID da ke Najeriya har zuwa lokacin da za a kammala shari’a.
Kotun ta bada wannan umarnin ne a yau Alhamis, bayan da wadanda aka gabatar a gaban kotun suka masa laifin da ake tuhumar su da shi.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a kotu, kuma suka masa laifuka 11 da ake cajin su da laifin aikatawa.
Wadanda ake zargin sun hada da Muhammad Kuchazi, wanda aka ce shi ne daraktan kasuwanci na P&ID a Tsibirin British Virgin Islands, sai kuma Adamu Usman, wanda aka ce shi ne darakatan masana’antu a nan Najeriya, na kamfanin P&ID.
Biyo bayan bayanan da EFCC ta gabatar wa kotu da kuma amsa laifukan su da suka yi, an kama Usman da aikata laifuka 11, shi kuma Kuchazi laifuka 10.
Dukkan laifukan 11 sun danganci karkatar da kudade, rashin bin ka’idar aikinn ofis da kuma yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.
Lauyan da ke wakiltar EFCC mai suna Bala Sanga, ya yi wa kotu nunin cewa, “a inda aka gurfanar da kamfani har aka fara cajin sa, to kotu za ta bada umarnin a rike kadarorin sa har zuwa lokacin da za a kammala shari’a, a ga yadda za ta kaya tukunna.”
Mai Shari’a Edward Ekwo, bayan ya yi dogon bayani tare da kawo wasu hujjoji, sai ya bada umarnin gwamnatin tarayya ta rike kadarorin P&ID da ke Najeriya, har zuwa lokacin kammala shari’a.
EFCC ta fara binciken masu hannu cikin harkallar gas, wadda a yanzu ke neman janyon wa Najeriya asarar dimbin kudade har naira tiriliyan 3.2.
Discussion about this post