An damke daya daga cikin zaratan sojojin musamman da aka tura a Karamar Hukumar Munguno, bisa zargin aikata fashi da kuma kwacen mota a Yola, Jihar Adamawa.
Ana zargin sojan da aikata laifin ne tare da wani farar hula, kamar yadda Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje ne ya bayyana cewa al’amarin ya faru a ranar Talata misalin karfe 1 na dare, a Yola, jihar Adamawa.
“Ana zargin shi da wani abokin sa farar hula da bin wata mata wadda ke tuka Toyota Camry, sai da aka je daidai ‘Target Junction’, sannan suka nuna ta da bindiga, suka ce ta fice daga motar. Ita kuma ta fita.
“Amma sai aka yi sa’ar kai rahoton satar ga ‘yan sandan da ke aiki kusa da inda aka yi fashin, inda su kuma tare da hadin bakin ‘yan sintiri, suka damke wadanda ake zargin.
“Mun yi nasarar gano motar a hannun su, kuma mun samu bindiga samfurin AK47 da kuma harsasai 35 daga gare su.” Haka Nguroje ya bayyana.
Da ya ke amsa tambaya daga manema labarai, sojan ya amsa laifin sa tare da bayyana sunan sa Dampa Hyellambamun.
Ya kara da cewa an turo shi wani aiki ne daga sansanin su da ke Munguno zuwa Yola. Amma kuma tun ranar 10 Ga Agusta wa’adin komawar sa Munguno ya cika, ya ki komawa.
“An damka min bindiga, amma babu albashi, babu alawus. Shin ya ku ke so na yi a lokacin da na kai gargarar tsananin fatara da yunwa? An shafe watanni ba a biya mu ba.” Inji shi.