Mataimakiyar Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana wa manema labarai cewa akwai masu son dawowa Najeriya har su 649 daga Afrika ta Kudu.
Ta yi wa Kwamitin Majalisr Dattawa wannan bayani ne a lokacin da ta masar gayyatar jin bin ba’asi daga kwmitin kula da mazauna kasashen waje, a jiya Litinin.
Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki kadan bayan da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya yi irin wannan ganawa da wannan kwamiti.
Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya tura Jakada na Musamman, Ahmed Abubakar zuwa Afrika ta Kudu, domin ganawa da Shugaba Cyril Ramophosa.
Tuni dai Abubakar ya dawo, kuma ya shaida wa Buhari abin da ganawar da ya je da shugaban Afrika ta Kudu ta kunsa.
Shi ma Shugaba Buhari ya bada odar gaggauta dawo da duk wani mai son dawowa zuwa gida Najeriya.
Tuni dai jirgin Kamfanin Peace Air, ya yi balantiyar dawo da masu son dawowa, duk da dai an samu tsaiko saboda rashin ingantattun takardun fasfo na wasu maso son dawowar.
Amma duk da haka ta ce nan ba da dadewa ba za a dauko a dawo da su gida.
“Maganar nan da na ke da ku a yanzu haka, akwai ‘yan Najeriya 640 da suka yi rajistar sunayen su cewa su na son dawowa don kan su. Kuma mun tabbatar cewa za a kara samun masu bukatar dawowa din.
“Jirage biyu ne za su dawo da su. Idan muka dawo da wadannan 640 na farko din, sannan kuma za musan yawan wadanda za su biyu bayan su, na masu bukatar dawowar.
Jakadan Najeriya a Afika ta Kudu ya ce sama da ‘yan Najeriya 500 ne ke son dawowa daga gobe Laraba mi zuwa.
Dabire ta ce za a shirya takardun gaggawa ga wadanda takardun iznin zaman kasar ya kare, sannan kuma sun a sauka za a fara koyar da su sana’o’in hannu domin samun sana’ar dogaro da kan su.