ASHURA: ‘Yan Sanda sun kashe ‘Yan Shi’a 12 – IMN

0

Kungiyar Harkar Islamiyya (IMN), ta yi ikirarin cewa ‘yan sanda sun kashe mata mabiya 12 a garuruwa daban-daban a yau Talata wajen muzaharar Ashura.

Musulmi mabiya Shi’a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar muzaharori a fadin kasar nan. Hakan kuwa ya kasance duk da gargadin da Shugaban ‘Yan Sanda na Kasa, Mohammed Adamu ya bayar cewa an haramta musu yin zanga-zangar.

Sai dai kuma IMN ta bayyana cewa an kashe wasu mambobinb ta a kokarin da jami’an tsaro suka yi don murkushe zanga-zangar.

A yau Talata ne dai hukumar tsaro ta ‘yan sanda ta bayyana cewa za ta fassara wannan zanga-zanga a matsayin “taron gangamin shirin ta’addanci”.

Ashura rana ce da mabiya Shi’a ke gangamin nuna alhini da jimamin kisan Hussain (AS), jikan Annabi Muhammadu (SAW).

Mabiya Shi’a sun bayyana cewa an kashe mambobin su 12 a fadin kasar nan.

Kakakin IMN, Ibrahim Musa ne ya bayyana haka a yau Talata, inda ya bayyana cewa an kashe mabiya Shi’a a garuruwan Kaduna, Bauchi, Sokoto da Katsina.

Sanarwar dai ta ci gaba da cewa an gudanar da irin wannan zanga-zanga a Abuja, Jos, Kebbi, Minna, Lafiya, Yola, Gusau, Zariya, Kano, Jalingo, Damaturu, Hadeja da Fatiskum, kuma a na su bangaren lami lafiya suka gudanar da muzaharar.

Har yanzu dai ‘yan sanda ba su bayyana adadin wadanda ake zargin sun kashe ba.

IMN ta ce an kashe mutane uku, wasu uku a Gombe da Kaduna an kuma kashe mutum daya a Illela, Jihar Sokoto, wani daya ma an kashe shi a Malumfashi, Jihar Katsina.

Sanarwar da IMN ta fitar ta kuma yi tir da Sufeto Janar nan ’Yan Sanda, Adamu bisa abin da ta kira kokarin san a shan jinin mabiya El-Zakzaky.

Share.

game da Author