Osinbajo zai kaddamar da Sabon Tsarin Kiwon Dabbobi

0

A yau Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo zai kaddamar da Sabon Tsarin Kiwon Dabbobi a Jihar Adamawa.

Shirin mai suna ‘National Livestock Transformation Plan (NLTP), za a kaddamar da shi ne domin samar da mafita daga matsalolin rikice-rikice da kashe-kashen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma.

Shiri ne na gwamnatin tarayya da zai fara daga mataki na farko, daga 2019 zuwa 2028, tare da hadin guiwar jihohi a karkashin inuwar Hukumar Inganta Tattalin Arziki.

Ana son fara shirin ne domin ingantawa da habbaka fannin kiwo ta yadda zai rika samar da kudaden shiga, ta hanyar fara shi a jihohi bakwai da suka hada da: Adamawa, Benue, Kaduna, Filato, Nasarawa, Taraba da Zamfara.

Sai dai kuma idan ba a manta ba, an samu rashin fahimta a lokacin da aka yi kokarin kafa shirin RUGA, inda Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ya nesanta ofishin sa daga hakkin kula da shirin.

Sannan kuma Osinbajo ya ce RUGA da NLTP daban su ke, kowanne zaman kan sa ya ke yi.

Kwanaki kadan bayan bayanin da Osinbajo ya yi ne kuma sai Buhari ya dakatar da shirin RUGA.

Kaddamar da wannan shiri da ake kan yi a yau Talata a Adamawa zai kawo jihar a matsayin ta farkon fara amfani da wannan shiri, domin kawo karshen fadace-fadacen makiyaya da manoma.

Sannan kuma akwai manufa ta samun kudaden shiga da inganta harkar kiwo domin samar da sabbin dabarun yalwata yawan dabbobi, killace su, samar da masana’antun sarrafa madara da kuma naman shanu.

Share.

game da Author