SHARI’AR ATIKU DA BUHARI: Kotu ta bayyana ranar yanke hukunci

0

Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, ta bada sanarwar cewa gobe Laraba, 11 Ga Satumba ne za ta yanke hukuncin shari’ar da ake tabkawa tsakanin dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma Shugaba Muhammadu Buhari.

Shari’ar ta biyo bayan karar rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da Atiku ya ki amincewa da shi.

Hakan ce ta sa shi jam’iyyar PDP suka shigar da Buhari da kuma jam’iyyar APC kara kotu.

Kakakin Yada Labarai ta Kotun Daukaka Kara, Sa’adiya Kachalla, ta fitar da sanarwa kamar haka:

“Kotun Sauraren Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa za ta zartas da hukunci gobe Laraba, 11 Ga Satumba.” Haka ta bayyana a ranar Talata.

Idan aka yanke hukunci gobe Laraba, duk wanda hukuncin da aka yanke bai gamsar da shi ba, zai iya daukaka kara zuwa zuwa Kotun Koli.

A yanzu dai karar da PDP ta maka APC kadai ce ta rage a kotu, bayan sauran jam’iyyu uku da suka maka APC da Buhari kotu ba su yi nasara ba.

PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben 2019, tare da argin cewa APC tada baki da INEC, wato Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, domin a yi magudin zabe.

The party questioned Mr Buhari’s academic qualification.

Jam’iyyar PDP ta gabatar da shaidu 62, yayin da Buhari da APC ta gabatar wa kotu da shaidu bakwai.

Share.

game da Author